Gwamnan Jihar Osun Na Shirin Rage Kwanakin Aiki Domin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur
- Gwamnan jihar Osun na shirin sauƙaƙawa al'ummar jihar biyo bayan tsige tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan
- Gwamna Ademola Adeleke na shirin rage kwanaki da lokutan zuwa aiki a jihar domin tallafawa mutanen jihar
- Gwamnan zai kuma samar da motocin hawa ga al'ummar jihar duk a cikin shirin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya bayyana cewa shirin bayar da tallafi ga al'ummar jihar na nan tafe domim rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Jaridar The Cable tace gwamnan na kuma duba yiwuwar rage kwanaki da lokutan zuwa aiki a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar a ranar Juma'a, Adeleke ya ɗauki wannan alƙawarin ne ga al'ummar jihar a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a birnin Osogbo.
Bayan cire tallafin man fetur da aka yi, wasu jihohi da suka haɗa da Kwara da Edo, sun ɗauki matakai domin rage raɗaɗin ƙarin kuɗin ababen hawa ga ma'aikatansu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tallafin zai kawo sauƙi kan cire tallafin man fetur da aka yi, gwamna Adeleke
Adeleke ya bayyana cewa tallafin zai rage wahalar da cire tallafin man fetur ya janyo, inda ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki bisa manufofin jam'iyyar da alƙawuran da ya ɗauka lokacin zaɓe.
"Gwamnatin jihar Osun nan bada daɗewa ba za ta kawo motocin zirga-zirga da mutane za su riƙa amfani da su. Muna aiki kan rage lokacin aiki da ranakun aiki. Muna son mutanenmu su samu sauƙin rayuwa ta yadda za su ji daɗi." A cewarsa
Gwamnan ya kuma tabbatarwa da shugabannin jam'iyyar da mambobinta cewa zai tafi da kowa a gwamnatinsa, babu wanda za a bari a baya.
Gwamnan Edo Ya Rage Kwanakin Zuwa Makaranta
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya rage kwanakin zuwa makarantun firamare da ƙaramar sakandire a jihar.
Gwamnan ya mayar da ranakun zuwa makarantun sun koma kwanaki uku a sati domin rage raɗaɗin cire tallafin mai da aka yi.
Asali: Legit.ng