"Ba Zan Karɓa Ba Sai Kin Duƙa" Miji Ya Umarci Matarsa a Bidiyo, Ya Ki Karban Abinci
- Wani ɗan Najeriya ya yi biris ya ƙi karban farantin abincin da matarsa ta kawo masa saboda ta tsaya tana miƙa masa a tsaye
- Magidancin ya gaya mata cewa shi ɗan gargajiya ne kuma ya zama dole ta duƙa kan guiwowinta idan zata ba shi abinci
- Ma'auratan sun sha dirama kan haka a wani gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata mata 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta duƙa kan guiwa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.
Wannan dirama da ta auku tsakanin ma'auratan na cikin wani ɗan gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin TikTok mai suna, @sasha_mac_reality.
Yadda abun ya faru tsakaninsu
Bidiyon ya nuna matar ta shiga ɗakin da mijin ke zaune ɗauke da abinci a Faranti sannan ta miƙa masa.
Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai nan take cikin ruwan sanyi da kalamai masu daɗi, mutumin ya gyara mata da cewa shi ɗan al'ada ne kuma ta san abinda ya kamata ta yi idan zata ba shi abinci.
Ba tare da jayayya ba, matar ta zube kasa kan guiwowinta, ta faɗi kalamai masu ratsa zuciya kamar yadda mijinta ya buƙata, daga bisani ya karɓi kwanon abincin.
Kali bidiyon abinda ya faru tsakanin mata da mijin
Bidiyon ma'auratan ya ja hankalin mutane da dama
MAGASCO BAMENDABOY ya ce:
"Kai amma wannan mutumin yana da abun dariya, ka siya mata duk abinda ta nema a rayuwar nan kuma ka nuna mata soyayya ɗan uwa, Allah ya maka albarka."
Skyz ya maida martani da cewa:
"A al'adar mu mata suna duƙa wa mazajensu amma har yanzun ina mamakin yadda muke ɗaukarsu da kulawa da ba su kulawa."
Hazikin Matashi Dan Najeriya Ya Sace Zuciyar Kyakkyawar Budurwa Cikin Minti 5, Hirarsu Ta Bada Mamaki
Atugonza Philomena ya ce:
"Ɗan gargajiya kuma kana cin abinda a ɗakin kwana, wurin da harkalla take faɗa wa, wannan cin mutuncin ɗakin kwana ne."
Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa
A wani labarin kuma Wani magidanci ya shiga ƙunci bayan Likita ya basu shawara shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7 watau mako ɗaya.
Sai dai mutumin bai ji daɗin wannan shawara ba domin ganinsa wannan jiran bai zama wajibi ba tunda dai an yi musu tsarin iyali, bidiyonsu ya ɗau hankali.
Asali: Legit.ng