Matashi Ya Nunawa Duniya Masoyiyarsa Baturiya Yayin da Ya Yi Nasarar Mallakarta

Matashi Ya Nunawa Duniya Masoyiyarsa Baturiya Yayin da Ya Yi Nasarar Mallakarta

  • Wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce bayan ya baje kolin masoyiyarsa tsohuwar baturiya a soshiyal midiya
  • A cewarsa, baturiyar ta ce ba za ta ba shi ko sisi ba har sai sun hadu ido da ido
  • Mutane da dama basu goyi bayan yadda ya nunawa duniya ita cike da alfahari ba inda suka caccake shi, wasu kuma sun yi masa ba'a

Wani matashi dan Najeriya ya garzaya dandalin TikTok domin baje koli masoyiyarsa wacce ta kasance dattijuwar baturiya.

Alamu sun nuna shi da matar sun hadu ne a soshiyal midiya kamar yadda ya bayyana cewa ta ce ba za ta tura masa kudi ba har sai sun hadu.

Matashi da masoyiyarsa baturiya
Matashi Ya Nunawa Duniya Masoyiyarsa Baturiya Yayin da Ya Yi Nasarar Mallakarta Hoto: @mimipeso021
Asali: TikTok

Matashin ya hadu da baturiyar

Ya wallafa hotunan da suka dauka tare da matar da ba a bayyana sunanta ba sannan ya rufe da wani hotonsa rike da daloli a hannu.

Kara karanta wannan

Sallah: Tsadar Raguna Ba Zai Hana Mu More Bikin Sallah Ba, 'Yan Najeriya Sun Magantu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake bayanin hoton dalan, matashin ya ce a karshe dai ta rabu da kudin nata. Wallafan da ya yi bai yi wa yan Najeriya da dama dadi ba inda suka caccake shi.

Kalli wallafarsa a kasa:

Jama'a sun yi martani

mA MI ta ce:

"Wannan matar da saurayina ke magana da ita abu kadan ka je ka kwaceta oo Allah."

GBOLEXY ya ce:

"Kai yanzu saboda dubu 80 ne ta zo ganinka, dukkanku ba za ku huta da kyau ba."

MABEL ya ce:

"Kuna bata aiki yallabai wannan ba abun dariya bane ka yi tunani turawa nawa ne za su ji labarin nan yanzu."

KCD ya ce:

"Haka kuke yi kuna bata kanku yanzu ya za ka ji idan yar'uwarka ta ga kana sanya Pat a matsayin Gara????"

totheworld ya ce:4"Zan yi nawa bidiyon wata mai zuwa..kowa ya zuba ido.

Kara karanta wannan

“Iyayena Sun Nemi Na Bar Masu Gidansu”: Matashiya Ta Koka Bayan Tsohon Saurayinta Ya Dankara Mata Ciki

"Aha babu ta inda kalaman karfafa gwiwa baya fitowa nima ina ta fargabar bari tawa ta zo amma kun bude mun idanuna."

"Yayata ke sa ni kwanciya da mijinta" Budurwa na dauke da cikin mijin yayarta, ta ki zubarwa

A wani labari na daban, jama'a sun yi Allah wadai da wasu iyali bayan miji ya dirkawa kanwar matarsa ciki.

Tun farko matar ce ta sa kanwarta kwanciya da mijinta saboda hana shi bin matan banza a waje sakamakon ciki da ke hana ta hada gado da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng