Wata Matar Aure, Maryam Hussaini Ta Nemi Rabuwa da Mijinta Saboda Rashin Kulawa

Wata Matar Aure, Maryam Hussaini Ta Nemi Rabuwa da Mijinta Saboda Rashin Kulawa

  • Dirama a Kotu yayin da wata matar aure, Maryam Hussaini, ta nemi a datse igiyoyin aurenta saboda mijin ba ya bata kulawa
  • Matar ta shaida wa Kotun cewa tun 2014 aka ɗaura musu aure kuma Allah ya basu 'ya'ya uku amma mijin baya kulawa da su
  • Alkali ya sake dage karar zuwa ranar 18 ga watan Yuli, domin a kai wa mijin sammaci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Wata matar aure mai suna Maryam Hussaini ta garzaya Kotun yanki da ke Kubwa a birnin tarayya Abuja, ta buƙaci Alkali ya raba aurenta da mijinta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Maryam ta zargi mijinta kuma uban 'ya'yanta da rashin kulawa da sauke haƙkinta da ke kansa da na 'ya'yan da Allah ya ba su.

Rikicin ma'aurata a Kotu.
Wata Matar Aure, Maryam Hussaini Ta Nemi Rabuwa da Mijinta Saboda Rashin Kulawa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Matar ta shaida wa Kotun cewa an ɗaura mata aure da mijinta kamar yadda shari'ar Addinin Musulunci ta tanada tun a shekarar 2014, shekaru 9 kenan da suka wuce.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Ta ce Allah ya albarkaci aurensu da samun ƙaruwar 'ya'ya uku amma mijin ya gaza kulawa da ita da kuma yaran da ta haifa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shin mijin ya halarci zaman Kotun?

Maryam ta faɗa wa Kotun cewa a ranar farko da aka sa domin fara zama kan ƙarar, 22 ga watan Yuni, wanda ake ƙara watau Mijinta ya halarci Kotun amma aka ɗaga ba tare da sauraron kowane bangare ba.

A jawabinta, Maryam ta gaya wa Kotun cewa:

"A ranar ƙarshe da aka ɗage zaman, 22 ga watan Yuni, 2023, mijina ya halarci Kotun nan amma Kotu ba ta zauna kan ƙarar ba aka ɗaga zuwa yau, yanzu ya yi fushi ya ce ba zai ƙara zuwa ba."

Kotu ta kara ɗage zaman domin aika wa mijin sammaci

Bayan sauraron jawabin matar, alkalin Kotun mai shari'a Yahaya Sheshi, ya ƙara ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Eid El Kabir: Portable Mai Wakar Zazu Ya Hargista Intanet Bayan Nuna Shanu 5 Da Raguna 2 Da Ya Siya Don Shagulgulan Sallah

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa Alkalin ya ɗauki wannan matakin ne domin ba da lokaci a kai wa wanda ake ƙara sammaci.

Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa

A wani labarin na daban kun ji cewa Wani mutumi ya shiga yanayin ƙunci bayan Likita ya shawarce shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7.

Bayan an musu tsarin taƙaita iyali shi da matarsa, kwararren likitan ya shawarci mutumin ya haƙura na ɗan wani lokacin kafin ya kwanta da matarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262