"Ku Ji Tsoron Allah" Malamai Sun Aike da Sako Ga Shugabannin Siyasa
- Malamai da limaman jihar Ogun sun yi kira ga sabbin shugabanni su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin amanar da ke kansu
- Wannan kira na kunshe a sakon barka da sallah mai ɗauke da sa hannun sakataren kungiyar Shaykh Tajudeen Adewunmi
- A cewar malaman ya kamata 'yan Najeriya su kwankwaɗi romon ayyuka da tsarukan da zasu tsamo su daga talauci sakamakon sadaukarwan da suka yi
Ogun State - Ƙungiyar Malamai da limamai reshen jihar Ogun ta roƙi shuwagabannin siyasa su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da Allah ya ɗora musu bayan lashe zaɓe.
Rahoton jaridar Daily Trust ya ce shugaban ƙungiyar, Shaykh Sikirullahi Babalola, ne ya faɗi haka ranar Laraba a cikin saƙon barka da Sallar layya (Eid-El-Kabir).
Sakataren ƙungiyar, Shaykh Tajudeen Adewunmi, ne ya fitar da sanarwan ranar idi 10 ga watan Zul Hijjah, 1444H wanda ya yi daidai da 28 ga watan Yuni, 2023.
Ya ce kowane ɗan ƙasa na da gudummuwar da zai bada wajen gina ƙasa yayin da aka rantsar da sabbin shugabannin da zasu jagoranci ƙasar nan kusan wata ɗaya kenan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Malamin, suna roƙon shugabanni da sauran 'yan siyasa da su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin amanar da talakawansu suka ɗora masu.
A ruwayar Daily Post, ya ce:
"Ya kamata su gaggauta lalubo hanyar warware talaucin da ke ƙara lulluɓe mutane, rashin tsaro, faɗuwar tattalin arziƙi, lalacewar ilimi, ƙarancin ayyukan raya ƙasa da sauran kalubalen da suka dabaibaye Najeriya."
"Babu tantama 'yan Najeriya suna aiki tuƙuru da jajircewa, abinda suke fata kaɗai shi ne Allah ya basu jagorori masu mutunci domin dawo da ƙasar nan kan ganiyarta."
"Ya kamata sadaukarwan da 'yan ƙasa suka yi su samu sakamakon manyan ayyuka da tsare-tsaren da zasu yi tasiri wajen yaye masu wahalhalun da su ke fama da su duba da arziƙin da Allah ya ba ƙasar nan."
Eid-el-Kabir: Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Yan Najeriya Su Yi Wa Shugabanni Addu'a
A wani labarin na daban kun ji cewa Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su dage da yi wa sabbin shugabanni Addu'o'i kuma su mara masu baya.
Jim kaɗan bayan dawowa daga wurin sallar idi babba, Alhaji Sa'ad Abubakar ya ce lokacin siyasa ya wuce, yanzu lokaci ne na shugabanci.
Asali: Legit.ng