"Muna Bukatar Yin Sadaukarwa" Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Bayan Gama Sallar Idi
- Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ja hankalin 'yan Najeriya jim kaɗan bayan kammala Salla a masallacin idi a jihar Legas
- Tinubu ya ce a fili yake akwai buƙatar hadaya da sadaukarwa domin Allah ba ya ɗora wa bawa abinda ya fi ƙarfinsa
- Ya kuma ƙara da rokon 'yan Najeriya su jingine banbancin da ke tsakaninsu su rungumi juna cikin soyayya da ƙaunar juna
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Lagos State - Shugaban ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya ja hankalin 'yan Najeriya da su ƙara ƙarfin imani da Allah SWT cewa wata rana ƙasar nan zata samu zaman lafiya mai ɗorewa.
Shugaba Tinubu ya yi wannan furucin ne ga 'yan jarida jim kaɗan bayan kammala sallar idi babba (Eid-el-Kabir) a filin idin barikin Dodan, jihar Legas, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya
Tinubu ya kuma jaddada bukatar haɗa kai da ƙaunar juna kana ya roƙi 'yan Najeriya su jingine duk wani banbancin addini ko ƙabila sannan su yi hadaya.
Allah ba zai ɗora wa Najeriya abinda ba zata iya ɗauka ba - Tinubu
The Nation ta ce a sanarwan da kakakin shugaban kasan, Dele Alake, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ƙara da cewa Allah ba zai ɗora wa kasar nan nauyin da ba zata iya ɗauka ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa bayan gama Sallar idi, Tinubu ya ce:
"Ina ƙara godiya ga Allah SWT wanda ya raya mu cikin ƙoshin lafiya har muka kawo yau kuma muna Addu'a ya ƙara bamu lafiya da kwanciyar hankali. Akwai muƙatar mu yi layya, wannan a bayyane yake."
"Amma Allah ba zai ɗora wa bawa nauyin da ba zai iya ɗauka ba, a koda yaushe Allah na nan tare da mu, ya zama wajibi mu ƙara imani da ƙasar mu. Mu Aminta da juna kana mu yarda cewa dole mu haɗa hannu wajen gina ƙasar mu."
"Ba bu zancen addini ko ƙabila, mu zauna da juna cikin farin ciki da nishaɗi. Zaman lafiya da kwanciyar hankali zai dawo a Najeriya kuma Allah zai sa komai ya wuce a yanzunan da ake fama."
Shugaba Tinubu Ya Gana da Buhari a Birnin Landan
A wani rahoton na daban kuma Shugaba Tinubu ya gana da magabacinsa, Muhammadu Buhari a Landan na kasar Burtaniya kafin dawowa Najeriya.
Tun ranar 20 ga watan Yuni shugaba Tinubu ya nufi kasar Faransa domin halartar taro, daga bisani kuma ya wuce Landan.
Asali: Legit.ng