Yawan Kudade Da Kuma Kasashen Da Ke Bin Najeriya Bashi, Bayan Tinubu Ya Karbi $500m Daga Bankin Duniya
- Najeriya na daga cikin kasashen duniya da suke yawan karban basuka daga kasashe da dama
- Na kwanan nan shi ne wanda Bankin Duniya ta amince da ba da bashin $500m ga kasar Najeriya
- Wannan shi ne karo na biyu da sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke karban bashi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Bankin Duniya a ranar Litinin 26 ga watan Yuni ta sanar da cewa ta amince da ba wa Najeriya sabon bashi na $500m.
A cikin sanarwar da bankin ta fitar, ta ba da bashin ne saboda inganta rayuwar mata a kasar.
Rahotanni sun tabbatar cewa wannan shi ne karo na biyu da bankin ke ba da bashin a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu, Legit.ng ta tattaro.
Wani bangare na sanarwar a cewar gidan talabijin na Channels na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bankin Duniya ta amince da bashin $500m ga Najeriya don inganta rayuwar mata.
"Wannan tallafi zai taimakawa gwamnatin Najeriya wurin zuba kudade don inganta rayuwar mata a kasar."
Yawan basussukan da kasashe ke bin Najeriya daga watan Maris 2023
1. China (Bankin Exim na China): $4.34bn
2. Faransa: $593.75m
3. Japan: $62.02m
4. India (Bankin Exim na India): $26.64m
5. Jamus: $144.75m
Jerin hukumomin da suke bin Najeriya bashi daga watan Maris 2023
1. Kungiyar Cigaban Kasa da Kasa: $13.84bn
2. Bankin Kasa da Kasa da Gyare-gyare: $4885.35m
Gamayyar Bankunan Cigaban Afirka
1. Bankin Cigaban Afirka: $1.57bn
2. Tallafin Afirka: 19.97m
3. Kudin Tallafin Cigaban Afirka: 972.55m
Sauran hukumomin kasa da kasa da ke bin Najeriya bashi bayan Tinubu ya karba karo na biyu
1. Bankin ba da tallafi ta IMF: $3.30bn
2. Bankin Larabawa don Cigaban Afirka: $5.34m
Magana Ta Kare, Sanata Ya Faɗi Mutum 2 Tal da Suka Jawo Atiku Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Zaɓen 2023
3. Tallafin Cigaban Nahiyar Turai: $37.74m
4. Bankin Musulunci: 144.12m
5. Tallafin Kasa da Kasa don Cigaban Noma: $ 272.30m
Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Bai Wa Dalibai Rance
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan ba wa dalibai bashi a kasar.
Wakilin shugaban, Dele Alake shi ya bayyana haka a fadar shugaban kasa a ranar Litinin a Abuja.
Ba wa daliban bashi a cewar gwamnatin zai taimaka musu wurin yin karatu cikin sauki.
Asali: Legit.ng