Kotun Shari'ar Musulunci A Kano Ta Daure Lauyan Bogi Watanni 15 A Gidan Kaso
- Kotun Shari'ar Musulunci da ke karamar hukumar Kiru ta jihar Kano ta daure lauyan bogi watanni 15 a gidan kaso
- Wanda ake zargin mai suna Zaharaddin Sani Maidoki ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da aka zayyana masa
- Alkalin kotun, Abdulmuminu Gwarzo ya daure shi watanni 15 a gidan kaso tare da biyan makudan kudade har N20,000
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - An gurfanar da wani lauyan bogi mai suna Zaharaddin Sani Maidoki a gaban kotun shari'ar Musulunci bisa zargin yaudara da cin amana.
Kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru da ke jihar Kano ta daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan kaso.
Kotun da ke Kano ta yanke wa lauyan bogin watanni 15 a gidan kaso
Wanda ake zargin wanda dan asalin jihar Kaduna ne ya bayyana kansa a matsayin lauya da niyyar kare wasu mutane a gaban kotu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zaharaddin ya amsa dukkan tuhume-tuhumen da ake kararsa akai wanda ya hada da bayyana kansa a matsayin dan jarida daga jihar Kaduna.
Alkalin kotun, Abdulmuminu Nuhu ya daure wanda ake zargin watanni 15 a gidan gyaran hali, Aminiya ta tattaro.
Hukuncin da Alkalin kotun ya yanke bai ba da damar biyan kudin tara ba, amma zai biya N20,000.
Yayin yanke hukuncin, Alkalin kotun ya daure matashin tare da yin amfani da dokokin shari'a ta jihar Kano karkashin sashe na 337.
Alkalin kotun ya kwace dukkan takardu da katin shaidar aiki
Kotun har ila yau, ta tura sako zuwa Kungiyar Lauyoyi ta jihar Kaduna don tabbatar da ikirarin shi lauya ne, inda kungiyar ta ce ba ta san da zamanshi a kungiyar ba.
Alkalin kotun ya shaida masa cewa yana da kwanaki 30 idan bai gamsu da hukuncin kotun ba zai iya daukaka kara.
Kano: Dahiru Yellow Ya Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shekaru 7 A Gidan Kaso Kan Zargin Safarar ’Yar Bayelsa Tare Da Musuluntar Da Ita
Kotun ta kuma kwace dukkan wasu takardu da ke tare da shi da kuma shaidar katin aiki da yake ikirarin shi lauya ne kuma dan jarida.
Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Daga Rushe Gine-Gine A Jihar
A wani labarin, kotu ta umarci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya dakatar da rusau da yake yi.
Wannan hukunci na zuwa ne bayan wani mazaunin Kano, Saminu Muhammad ya shigar da gwamnatin kara.
Alkalin kotun, S. A Amobeda a ranar 23 ga watan Yuni ya umarci gwamnan ya dakatar da shirin rushe shaguna a akan hanyar BUK.
Asali: Legit.ng