Dakarun Sojin Sama Sun Kai Samame Kan Mafakar 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno
- Sojin saman Najeriya (NAF) sun yi luguden bama-bamai kan mafakar 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno
- Majiyoyi sun bayyana cewa ruwan wutan sojin ya yi ajalin mayakan kungiyar da yawan gaske ranar Litinin, 26 ga watan Yuni
- Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin sabon hafsan NAF ya lashi takobin yaƙi da ta'addanci a ƙasar nan
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Borno State - Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta kaddamar da ruwan bama-baman lahira salamu alaikum kan mafakar mayaƙan kungiyar ta'addanci ISWAP a jihar Borno.
Rahoto ya nuna cewa luguden wutan NAF ya halaka mayaƙan ISWAP da yawan gaske kuma ya yi kaca-kaca da wuraren da suke samun mafaka.
Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da sabon hafsan sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal, Hassan Abubakar, ya lashi takobin farfaɗo da sojin sama a yaƙi da ta'addanci a kasar nan.
Yaushe NAF ta kai wannan samame?
Luguden wutan sojin saman ya gudana ne ranar Litinin, 26 ga watan Yuni, 2023 a wasu wurare da 'yan ta'adda ke sansani, waɗanda suka ƙunshi Andakar, Musari da Klabariya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dukkan waɗan nan wurare ukun na yankin Arewa maso Yammacin ƙaramar hukumar Marte a jihar Borno.
Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Tuwita ranar Talata.
Yadda NAF ta kai samamen da nasarar da aka samu
Wasu majiyoyi daga hukumar tattara bayanan sirri ta shaida wa Makama cewa Sojin sun kai samamen ne biyo bayan rahoton sirri da aka samu cewa wasu 'yan ta'adda sun shiga yankunan.
A cewar masanin, 'yan ta'addan sun gudo ne daga ruwan wutan sama da ƙasa da dakarun Operation Hadin Kai ke kai musu a yankunan Jubularam, Kwalaram da Sabon Tumbu.
"A lokacin da jirgin yaƙin NAF ya isa wurin da aka samu labarin taruwar yan ta'addan, an hangi mayakan ISWAP ɗin na yunkurin guduwa bayan ganin zuwan jirgin."
Nan take jirgin ya saki ruwan bama-bamai kuma bisa sa'a suka tashi a kan abin hari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ta'adda da yawa kuma ya lalata abin hawa da kayan aikinsu.
Majiyar ta ƙara da cewa, jirgin sojin saman bai tsaya nan ba, ya bi bayan wannan da wasu hare-haren luguden wuta a Musari da Klabariya, nan ma ya tura yan ta'adda da dama barzahu.
Hukumar DSS Ta Tona Shirin ‘Yan Ta’adda a Lokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya
A wani rahoton na daban kuma Hukumar DSS ta ankarar da al’umma cewa akwai shirye-shirye da wasu miyagu su ke yi na kai wa wuraren bauta da filayen wasanni hari.
An tattaro cewa ana yunkurin kai hare-haren ne a lokuta da kuma kafin bukukuwan babbar sallah.
Gwamna Zulum Ya Nuna Takaicinsa Kan Kisan Manoma a Borno, Ya Bayyana Kwakkwaran Matakin Da Zai Dauka
Asali: Legit.ng