'Yan Arewa Sun Roki Musulmai Su Yafe wa Shettima Kan Kalamansa, Sun Yaba Nagartar da Dattakunsa

'Yan Arewa Sun Roki Musulmai Su Yafe wa Shettima Kan Kalamansa, Sun Yaba Nagartar da Dattakunsa

  • A baya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi wata katobara a yayin wani taro da 'yan majalisun Tarayya
  • Shettima bayan katobarar ya nemi afuwar al'ummar Musulmi inda ya ce shi dan Adam ne kuma ajizi
  • Kungiyar NEPC ta roki al'ummar Musulmi da su yafewa mataimakin shugaban kasar saboda dattakun da ya nuna

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Kungiyar Gamayyar Ci Gaban Arewa maso Gabas (NEPC) ta roki al'ummar Musulmi su yafe wa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima kan kalamansa.

Kungiyar ta ce Shettima ya nemi afuwar al'ummar Musulmi saboda haka ya cancanci a yafe masa.

NEPC ta roki Musulmai su yafewa Kashim Shettima kan kalamansa na shugabancin majalisa
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Asali: Facebook

Kwadinetan kungiyar, Muhammed Konto Mafa shi ya yi wannan roko inda ya ce Shettima mutum ne mai nagarta musamman yadda ya roki gafarar Musulmi, cewar Daily Trust.

NEPC ta bayyana irin nagartar Kashim Shettima da kan-kan da kai

Kara karanta wannan

Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Saboda kan-kan da kai da dattaku da kuma kwarewa na shugabanci, Kashim Shettima ya nemi afuwar al'ummar Musulmi.
"Ba ya yi haka ba ne saboda ya yi kuskure gaba daya, ya yi haka ne saboda yadda yake mutunta fahimtar mutane.
"'Yan Najeriya, musamman Arewa ya kamata su sani cewa Kashim Shettima mutum ne mai daraja ba zai yi wani abu da ya sabawa mutanen shi ba.
"Dukkan mu 'yan Adam ne ya kamata mu duba kyawawan halayen mataimakin shugaban kasar, duk dan Adam ajizi ne."

Kalaman Shettima sun jawo cece-kuce a tsakanin al'ummar Musulmi

Idan ba a manta ba, Kashim Shettima a wani taro ya bayyana goyon bayansa ga lalataccen Kirista dan Kudu akan Musulmi dan Arewa mai nagarta a shugabancin majalisar dattawa.

Shettima a yayin taron ya ce:

"A wannan yanayin da muke ciki, lalataccen Kirista dan Kudu ya fi cancanta akan nagartaccen Musulmi dan Arewa ya shugabanci majalisar dattawa a Najeriya."

Kara karanta wannan

‘Zagin Annabi’: Shehin Malamin Musulunci Ya Yi Magana Kan Kisan da Aka Yi a Sokoto

Wannan magana da Kashim Shettima ya yi, ya jawo kace-nace a cikin al'ummar Musulmi.

Yayin da daga bisani mataimakin shugaban kasar ya nemi afuwar al'ummar Musulmi bisa wadannan kalamai nasa.

Kashim Shettima Ya Nemi Afuwa Kan Kalaman Da Ya Yi

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya nemi afuwar Musulmi kan kalamansa

Shettima ya yi wasu kalamai da ba su yi wa al'ummar Musulmi dadi ba dangane da zabukan majalisar dattawa.

Shettima ya nemi afuwar Musulmi akan kalamansa inda ya ce ba a fahimce shi ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.