Gwamna Obaseki Ya Ba Dalibar da Ta Kafa Tarihi a Jami'ar LASU Aiki
- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ɗauki dalibar da kafa tarihin da ba'a taɓa ba a jami'ar LASU, aiki kai tsaye
- Obaseki ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki Aminat Yusuf aiki ne domin toshe kowace ƙofa ga wasu jihohi da ka iya ɗauke ta
- Misis Aminat ta kammala digirinta na farko da daraja mafi kololuwa 5.0 a fannin ilimin sanin doka (Low) a jami'ar jihar Legas
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Edo State - Gwamnna Godwin Obaseki na jihar Edo ya miƙa tayin ɗaukar aiki kai tsaye ga Misis Yusuf Aminat, wacce ta kafa tarihin gama karatu da daraja mafi gurma a jami'ar jihar Legas (LASU).
Bayan samun nasarar gama digirin farko a fannin ilimin doka (Law) da maki 5.0 CGFA wanda babu sama da shi, Aminat ta kafa tarihin zama ɗalibar da ba'a taɓa kamarta ba a tarihin jami'ar LASU.
"Ya Daina Nuna Mun Soyayya" Wata Mata Ta Roki Kotu Ta Raba Auren Kuma Ta Umarci Mijin Ya Riƙa Biyanta N30,000
Jami'ar ta kai shekara 40 da kafuwa kuma tun wannan lokaci ba a taɓa samun dalibin da ya gama digirin farko da makin da Yusuf Aminat ta kammala ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Gwamna Obaseki ya ɗauki Yusuf Aminat aiki
Da yake zantawa da 'yan jarida a Benin, babban birnin jihar Edo, gwamna Obaseki ya bayyana cewa jihar, wacce Aminat ta fito, ta yanke ba zata tsaya iya taya murna kaɗai ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce gwamnatinsa ta miƙa mata tayin ɗaukar aiki kai tsaye ne domin gudun kada Edo, "Ta yi gangacin bari wasu jihohin su ɗauke ta."
"Ba ta kammala aikin bautar ƙasa ba, saboda haka abinda zamu yi yanzu shi ne zamu rubuta takardar roƙo ga hukumar kula da matasa 'yan bautar kasa (NYSC) domin a turo mana ita nan gida jihar Edo."
Gwamna Zulum Ya Nuna Takaicinsa Kan Kisan Manoma a Borno, Ya Bayyana Kwakkwaran Matakin Da Zai Dauka
"Ta haka ne kaɗai zamu toshe kowace ƙofa don kar mu rasa ta."
Da yake tsokaci kan shirinsa na karfafa ɓangaren aiki a jihar Edo, gwamna Obaseki ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta shirya inganta nagartar ma'aikata a jihar Edo.
Sabbin Hafsoshin Tsaro da IGP Zasu Dawo da Zaman Lafiya a Filato, Mutfwang
A wani rahoton na daban kuma Gwamna jihar Filato ya ce sabbin hafsoshin tsaro ka iya share wa Najeriya hawayenta game da matsalar rashin tsaro.
Ya ce yana da yaƙinin cewa suna da gogewar da zasu iya magance matsalar tsaron da ta addabi jihar Filato da Najeriya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng