Kano: Wani Ya Maka Makwabcinsa A Kotun Shari'ar Musulunci Kan Sare Bishiyar Gidansa, Ya Nemi A Biya Diyya
- Wani mazaunin karamar hukumar Kiru ya maka makwabcinsa a kotun shari'ar Musulunci bisa zargin sare bishiyar gidansa
- Wanda ke karar, Zubairu Yako ya ce Isa Kofa Yako ya sare bishiyar gidansa a shekarar 2013 ba tare da neman izininshi ba ko yafiya
- Isa Kofa Yako ana shi bangaren ya ce ya sare bishiyar ne bayan wani ya bashi izini duk da cewa ba gidansa ba ne
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Wani mutum mai suna Zubairu Yako ya maka makwabcinsa a gaban kotun shari'ar Musulunci da ke jihar Kano bisa zargin sare bishiyar gidansa.
Wanda yake karar ya ce makwabcinsa Isa Kofa Yako ya sare bishiyar gidansa a shekarar 2013 saboda haihuwar matarsa ba tare da izini ba.
Ya ce abin da yafi bashi haushi shi ne yadda bai zo ya nemi afuwar aikata hakan ba, shi yasa yake neman ya biya diyyar saran bishiyar da ya yi, Daily Trust ta tattaro.
Makwabcin ya tabbatar da cewa ya sare bishiyar da izinin wani mutum
Da kotun da ke zamanta a karamar hukumar Kiru ta tambayi wanda ake zargin, ya tabbatar da cewa ya sari bishiyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa kafin ya sare bishiyar sai da ya tambayi izini a wurin wani duk da cewa ba gidansa ba ne.
Alkalin kotun, Abdulmumini Nuhu Gwarzo ya dage sauraran karar har zuwa bayan Sallah don ci gaba da zaman kotun.
Wanda ke karar ya koka saboda kin neman afuwa da makwabcin nasa ya yi
Da yake hira da 'yan jaridu bayan zaman kotun, wanda ke karar ya ce:
"Ina jiransa tsawon wannan lokaci ya zo ya nemi gafara saboda ya shiga gidana ya sari bishiya don haihuwar da matarsa ta yi.
"Abin haushi shi ne bai zo ya nemi afuwa ba kuma a lokacin bai nemi izini na ba."
Rashin Daraja: Magidanci Ya Maka Surikansa Kara a Gaban Kotun Shari'ar Musulunci a Jihar Kano Kan Abu 1 Rak
Rahotanni sun tattaro wanda ake karar yana cewa:
"Wani ne ya bani izinin sarar bishiyar duk da cewa ba gidansa ba ne.
"Amma shekaru 10 yanzu ban san me yake jira in zo in ba shi hakuri ba, idan yana son na biya shi ne zan biya."
Kotu Ta Umarci Abba Gida Gida Ya Dakatar Da Rushe-Rushen Gine-Gine A Jihar
A wani labarin, kotu ta ba da umarnin dakatar da rushe-rushe da gwamnatin Kano ke ci gaba da yi.
Saminu Muhammmad wanda ya shigar da gwamnatin kara kotu ya bukaci kotun ta hana gwamantin Kano rusa masa shagunansa.
Alkalin kotun, S.A Amobeda ya umarci gwamnatin ta dakatar da duk wani shiri na ci gaba da rushe dukiyoyin jama'a.
Asali: Legit.ng