An Shiga Tashin Hankali Yayin Da Yan Bindiga Suka Yi Wa Shugaban 'Yan Banga Kisan Gilla A Katsina

An Shiga Tashin Hankali Yayin Da Yan Bindiga Suka Yi Wa Shugaban 'Yan Banga Kisan Gilla A Katsina

  • 'Yan bindiga da ake tunanin 'yan ta'addan daji ne sun kashe Malam Nabange, shugaban 'yan bangan yankin Danmusa da ke jihar Katsina
  • An ce 'yan ta'addan, waɗanda suke ɗauke da manyan makamai, sun yo gayya ne ta musamman domin kashe shugaban 'yan bangan
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Sadiq Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin

Katsina - Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan ta'addan daji ne sun yi wa wani shugaban 'yan banga, Malam Nabange, kisan gilla.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi, inda 'yan ta'addan suka zo har gidan shugaban 'yan bangan, dake ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina suka halakashi.

Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan banga a Katsina
'Yan ta'addan daji sun yi wa shugaban 'yan banga kisan gilla a Katsina. Hoto: Mobile Media Crew
Asali: Facebook

'Yan ta'addan sun zo ne musamman don kashe shugaban 'yan bangan

Wani daga cikin 'yan bangan yankin da aka bayyana sunansa da Murtala, ya shaidawa jaridar Vanguard cewa 'yan ta'addan sun zo ne musamman domin kashe Nabange, duk da a yayin farmakin, sun harbi ƙarin wasu mutane biyu.

Kara karanta wannan

Maciji Ya Kashe Hatsabibin Babban Kwamandan ISWAP A Dajin Sambisa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa 'yan ta'addan sunzo ne da yawa ɗauke da muggan makamai, inda kai tsaye suka yi wa gidan shugaban 'yan bangan ƙawanya.

Ya ce sun ɗauki lokaci suna musayar wuta, kafin daga bisani harsashen bindigar Malam Nabangen su ƙare, inda daga nan ne suka ci ƙarfinsa, suka halaka shi duk kuwa da cewa bindigar ta su ba ta yi tasiri a kansa ba.

'Yan ta'addan sun cinnawa gidan wuta, sun tafi da mata uku

Murtala ya ƙara da cewa bayan haka 'yan ta'addan sun bankawa gidan wuta, sannan kuma suka tafi da wasu mata guda uku, waɗanda daga bisani kuma suka sako su.

Sannan Murtala ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun aikata wannan ɗanyen aikin ne a kan Nabange, saboda jagorantar 'yan banga da ya yi a kwanakin baya, inda aka yi wa 'yan ta'addan ta'asa mai yawa.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Hatsabiban 'Yan Ta'adda 6 Sun Sheƙa Lahira a Arewacin Najeriya

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ASP Sadiq Abubakar ya bayyana cewa ba su samu labarin farmakin ba sai ƙarfe 06:00 na safe, sakamakon ruwan sama da ya hana a iya sanar da su ta wayar tarho.

Ya ƙara da cewa jami'ansu sun bazama cikin dajin domin gano gami da kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Jihar ta Katsina dai na fama da ƙalubalen hare-haren 'yan ta'adda, wanda ko a watan Maris da ya gabata, sun kashe aƙalla mutane ashirin da biyu a Majifa, wani ƙauye da ke a ƙaramar hukumar Kankara a jihar ta Katsina.

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 4 a Bauchi

Wani labari da Legit.ng ta kawo muku a ƙarshen makon nan, kun ji cewa 'yan bindiga na cin karensu babu babbaka a wasu yankuna na jihar Bauchi.

Ko a ƙarshen makon nan, an samu labarin wani Farmaki da 'yan bindigar suka kai a yankin ƙaramar hukumar Ningi ta jihar, inda suka yi awon gaba da mutane huɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng