AEDC: Kamfani Ya Sanar da Sabon Farashi da Lokacin Ƙara Kuɗin Lantarki a Garuruwa 4
- Kamfanin AEDC ya fitar da sanarwar da tabbatar da cewa za a fuskanci tsadar lantarki a Najeriya
- Daga ranar 1 ga watan Yulin 2023, farashin da aka saba sayen wutar lantarki daga AEDC zai canza
- Sabon tsarin canjin kudin kasar waje da bankin CBN ya fito da shi ne ya jawo sauyin da aka samu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Kamfanin AEDC mai raba wutar lantarki a Abuja da kewaye ya tabbatar da cewa zai kara farashin da ake shan wuta saboda canjin kudin waje.
A rahoton The Cable, an samu labari AEDC wanda shi ne kamfanin da ke raba wuta zuwa birnin tarayya, Neja, Kogi da Nasarawa zai canza farashinsa.
Jawabin da kamfanin ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana cewa karin farashin ya zama dole ne a dalilin tangal-tangal da Naira take yi a kasuwar canji.
'Yan Maza Sun Kwanta: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Babban Farfesa a Najeriya Ya Koma Ga Mahaliccinsa
Bayan zaman Bola Tinubu shugaban kasa, bankin CBN ya bar farashin kudin kasashen waje a hannun ‘yan kasuwa, hakan ya karya darajar Naira.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar da AEDC ya fitar
"Daga 1 ga watan Yulin 2023, a sani cewa za a samu farashin shan wutar lantarki ya tashi sama a dalilin tangal-tangal a kasuwar canji.
A karkashin tsarin MYTO 2022, an tsaida Dalar Amurka ne a kan N441/$1, watakila yanzu dole a daidaita farashin zuwa N750/$1.
Hakan zai yi tasiri a kan farashin da ku ke shan wutar lantarki."
- AEDC
Nawa za a koma sayen wuta?
Daily Trust ta ce ‘yan rukunin B da C da ke samun wuta na awanni 12 zuwa 16 a rana, farashin da za su rika sayen kowane 1kWh zai N100 daga watan Yuli.
Su kuwa gidajen da ke kan rukunin wutar lantarki na A da B da ke yin awanni 16 zuwa 20 da lantarki za su rika biyan farashin da ya zarce N100/kWH.
Ga wadanda ba su amfani da na’urar auna shan wuta, daga Agusta za su ga kudin da za a rika yanko masu a wadannan garuruwa ya canza a dalilin haka.
Dole farashi ya lula sama
Tun a baya mu ka kawo rahoto cewa mutane su shiryawa tashin farashin lantarki na tsakanin 25% zuwa 40% daga ranar Asabar, 1 ga watan Yuli 2023
Yadda aka yi waje da tallafin fetur, hauhawar farashi da sauyin da aka samu a kasuwar canji za su haddasa karin tsadar lantarki a halin yanzu.
Asali: Legit.ng