Kano: Dahiru Yellow Ya Shaki Iskar ’Yanci Bayan Shekaru 7 A Gidan Kaso Kan Zargin Garkuwa Da ’Yar Bayelsa
- Dahiru Yunusa Yellow ya shaki iskar 'yanci bayan kammala wa'adinsa a gidan kaso na tsawon shekaru bakwai
- Ana zargin Yellow ne da yin garkuwa da Ese Oruru daga jihar Bayelsa zuwa Kano don musuluntar da ita da kuma auranta
- Kakakin hukumar gidan gyaran hali a Kano, Musbahu Lawan ya ce Yellow ya yi rayuwa mai nagarta yayin zamansa a gidan kaso
Jihar Kano - Dahiru Yunusa da aka fi sani da Yellow wanda aka yanke wa daurin shekaru 26 a gidan kaso ya samu 'yanci bayan shekaru bakwai a gidan kaso.
Ana zargin Yellow ne da safarar wata budurwa mai suna Ese Oruru wanda kotun daukaka kara ta yanke hukuncin a jihar Bayelsa.
Idan ba a manta ba, ana zargin Yellow da yin garkuwa da Ese Oruru daga jihar Bayelsa zuwa Kano da niyyar musuluntar da ita da kuma auranta, Daily Trust ta tattaro.
An bayyana Yellow a matsayin mutumin kirki yayin zamansa a gidan kaso
Kakikin hukumar gidan gyaran hali a Kano, Musbahu Lawan ya tabbatar da cewa Yellow ya kammala wa'adinsa na zaman gidan kaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa Yellow ya shiga makarantar sakandare na hukumar da ke cikin gidan gyaran halin.
A cewarsa:
"Bai taba yin fada da kowa ba, kuma bai taba karya wata doka ba a tsawon lokacin da ya ke nan, ya yi rayuwa mai nagarta abin koyi kuma kowa na mutunta shi anan.
Ana zargin Yellow da garkuwa da Oruru 'yar asalin jihar Bayelsa
An kama Yellow ne a jihar Bayelsa a shekarar 2015 tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 26 a gidan gyaran hali, cewar Leadership.
Alkalin kotun jihar, Jane Inyang shi ya yanke hukuncin inda ya ce Yellow bai amince da zarginsa da ake na safarar budurwar ba.
Sai dai wata kotun daukaka kara da ke zamanta a Port Harcourt ta saukaka zaman Yellow a gidan yarin zuwa shekaru bakwai.
Kotun Daukaka Kara Ta Rage Zaman Yunusa Yellow A Gidan Yari, Ta Fadi Ranar Da Zai Fito
A wani labarin, kotun daukaka kara da ke zamanta a Port Harcourt ta saukaka zaman Yellow a gidan yari zuwa shekaru bakwai.
Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Bayelsa a watan Mayu na shekarar 2020 ta yanke hukuncin daurin shekaru 26 kan Dahiru Yellow.
Asali: Legit.ng