An Yi Babban Rashi Yayin Da Tsohon Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kwanta Dama

An Yi Babban Rashi Yayin Da Tsohon Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Kwanta Dama

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi babban rashi na tsohon kakakinta kuma tsohon kwamishinan rundunar ƴan sanda
  • Frank Odita wanda ya riƙe muƙamin kakakin rundunar daga shekarar 1990 zuwa 1992 ya kwanta dama yana da shekara 84
  • Odita ya koma ga mahaliccinsa ne bayan ya yi ƴar gajeruwar jinya a asibiti inda ya ce ga garin ku nan a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Tsohon kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Frank Odita, ya kwanta dama yana da shekara 84 a duniya, rahoton The Cable ya tabbatar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya ce Odita ya mutu ne a yammacin ranar Juma'a a asibitin koyarwa na jami'ar Legas (LASUTH) bayan gajeruwar jinya.

Kara karanta wannan

Maciji Ya Kashe Hatsabibin Babban Kwamandan ISWAP A Dajin Sambisa

Tsohon kakakin rundunar 'yan sanda ya kwanta dama
Frank Odita ya bar duniya yana da shekara 84 Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Kafin ritayarsa daga aiki da rundunar ƴan sandan Najeriya, Odita shi ne kakakin rundunar daga shekarar 1990 zuwa 1992.

Sufeto Janar na ƴan sanda ya aike da saƙon ta'aziyyarsa

Adejobi ya bayyana cewa muƙaddashin Sufeto Janar, Kayode Egbetokun, ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Sufeto Janar na ƴan sanda Olukayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, a madadin jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya na miƙa ta'aziyya ga iyalai, ƴan'uwa da makusanta a bisa mutuwar tsohon kwamishinan ƴan sanda kuma kakakin rundunar, CP Frank Odita (Rtd.)."
"Shi ne kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya daga shekarar 1990 zuwa 1992, inda ya haɓɓaka dangantakar da ke tsakanin ƴan sanda da sauran al'umma."

Mamacin wanda ɗan asalin jihar Delta ne, ya yi ritaya daga aikin ɗan sanda a shekarar 1993, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Sabon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan, Ya Ɗauki Manyan Alkawurra

Odita shi ne shugaban kamfanin FrankCom Limited sannan kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙirƙiro shirin Security Watch Africa, wanda yake gabatarwa.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo Ya Kwanta Dama

A wani labarin kuma, al'ummar jihar Imo sun shiga jimami bayan tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dr Douglas Acholonu ya koma ga mahaliccinsa.

Acholonu, wanda yariman masarautar Orlu Gedegwum ne, ya mutu a safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Yunin 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng