“Nade-Naden Da Tinubu Ya Yi Na Gab Da Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya” – Gwamna Buni
- Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya bayyana babban abun da Najeriya za ta amfana daga nade-naden shugaban kasa Bola Tinubu
- Buni ya bayyana cewa rashin tsaro zai zama tarihi a Najeriya da wannan nade-nade da Tinubu ya yi na sabbin shugabannin tsaro
- Gwamnan na APC ya kuma ce sabon mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, zai yi amfani da gogewarsa wajen magance ta'addanci a Najeriya
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa nadin sabbin shugabannin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ya kara kusanta Najeriya zuwa ga ganin karshen matsalolin tsaronta.
Gwamnan ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da daraktan labarai da kula da harkokin labarai na jihar Mamman Mohammed ya gabatarwa manema labarai, jaridar Punch ta rahoto.
Buni ya magantu a kan nadi shugabannin tsaro da Ribadu a matsayin NSA da Tinubu ya yi
Da yake yaba masa musamman a kan sabon mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, Buni ya nuna karfin gwiwar cewa tsohon shugaban EFCC zai yi amfani da tarin gogewarsa wajen yakar rashin tsaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna Buni ya ce:
"Malam Nuhu Ribadu ya kasance kwararre wanda zai yi aiki tare da shugabannin tsaro don cimma manufar da aka sanya gaba.
"Shugabannin tsaron ma suna da gogewa da karfin gwiwar yar Najeriya wajen yaki da rashin tsaro a Najeriya."
Girman kan Shugaban kasa Bola Tinubu zai kai shi ga matsala, Inji Charly Boy
A wani labari na daban, mawakin Najeriya Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy ya yi martani a kan tsige shugabannin tsaro da nada sabbi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Charly Boy ya nuna rashin jin dadinsa ga yan Najeriya da suke jinjinawa shugaban kasar kan yadda yake tafiyar da harkokin gwamnati a baya-bayan nan.
Charly Boy ya kuma bayyana cewa duk abun da shugaban kasar ke yi don ya kawar da hankalin yan Najeriya ne a kokarinsa na cimma wani nufi nasa. Cewa duk so yake ya ga ya samu karbuwa a wajen yan kasar.
Asali: Legit.ng