Bankado Shirin Kai Hari Lokacin Babbar Sallah, CAN Ta Yi Martani Mai Zafi Ga Hukumar DSS

Bankado Shirin Kai Hari Lokacin Babbar Sallah, CAN Ta Yi Martani Mai Zafi Ga Hukumar DSS

  • Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta buƙaci hukumar DSS da ta duƙufa ts tashi tsaye ta yi aikinta yadda ya dace
  • CAN ta buƙaci hukumar da ta zahe damtse ta durfafi ƴan ta'adda a maimakon bayar da sanarwar cewa akwai barazanar tsaro lokacin shagulgulan
  • Ƙungiyar ta CAN tana martani ne kan sanarwar da DSS ta fitar cewa ƴan ta'adda na shirin kai hari a wuraren ibadah lokacin shagulgulan babbar Sallah

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) ta buƙaci hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) da ta durfafi ƴan ta'adda da masu aikata laifukan da ke addabar ƴan Najeriya, a maimakon bada gargaɗin yiwuwar kai hare-hare a lokacin shagulgula.

CAN ta bayyana cewa ya zama al'ada wajen DSS ta riƙa sanar da hakan inda ta buƙaci hukumar da ta tabbatar ta yi shirin kare duk wani hari da ƴan ta'addan ka iya kawo wa, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: FG Ta Fara Raba 'Solar' Kyauta A Fadin Ƙasar Don Rage Raɗaɗin Da Jama'a Ke Ciki

CAN ta yi gargadi ga DSS
Shugaban kungiyar CAN reshen jihar Kaduna, Rev. Joseph John Hayab Hoto: Dailypost.com
Source: UGC

Shugaban CAN reshen jihar Kaduna, Rev’d Joseph John Hayab, shi ne ya bayyana hakan lokacin da yake martani kan sanarwar da DSS ta bayar cewa ƴan ta'adda na shirin kai hare-hare a wuraren ibadah da wuraren shaƙatawa a lokutan shagulgulan babbar Sallah.

DSS ta saba aikewa da irin wannan gargadin lokacin shagulgula, a cewar Hayab

Hayab ya bayyana cewa wannan gargaɗin kamar na baya da hukumar ke aikewa ya saba zuwa ne lokacin da ake shirye-shiryen shagulgula, rahoton The Nation ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Muna fata da addu'ar cewa ba ɓadda kama bane. Hukumar DSS a matsayinta na hukumar sirri kamata ya yi ta cafko ƴan ta'addan ko miyagun kafin su ƙaddamar da shirinsu."
"Ƴan Najeriya sun sha wahala bai kamata a ƙara wahalar da su ba. Allah ya sanya an samu sabuwar gwamnati sannan an naɗa sabbin hafsoshin tsaro banda na DSS kawai."

Kara karanta wannan

Abdulrasheed Bawa: Me Yasa Har Yanzu DSS Ke Tsare Da Shugaban EFCC Da Aka Dakatar

Malamin addinin ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su so ganin an ɗauki ƙwararan matakai ba wai surutu ba kawai. Ya yi kira da mutane su kasance a ankare ta yadda da sun lura da wani abu za su sanar.

"Bayan wannan, tsaro ya rataya a wuyan kowa, yakamata kowa ya bayar da tasa gudunmawar wajen kawar da matsalar tsaro a ƙasar nan ta hanyar da ta dace ba farfaganda ba." A cewarsa.

CAN Ta Soki El-Rufai

A wani labarin kuma, ƙungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Ƙaduna, ta nuna ɓacin ranta kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai bisa kalaman da ya yi kan tikitin Muslim/Muslim.

Shugaban CAN na jihar, Rev Hayab ya bayyana cewa kalaman na El-Rufai ba su yi kama da halin musulmin ƙwarai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng