“Ya Fi Karfin Talaka”: Jami’ar Ambrose Alli Ta Kara Kudin Makaranta Da Kaso 300

“Ya Fi Karfin Talaka”: Jami’ar Ambrose Alli Ta Kara Kudin Makaranta Da Kaso 300

  • Gwamnatin jihar Edo ta kara kudin makaranta na jami'ar Ambrose Alli, Ekpoma, da fiye da kaso 300
  • Kungiyar daliban Najeriya Ta Kasa (NANS) ta caccaki gwamnatin jihar kan wannan mataki da ta dauka
  • Kungiyar daliban ta ce karin wani yunkuri ne na sanyawa ilimin jami'a ya fi karfin talakawa

Ekpoma, jihar Edo - Dalibai sun yi martani a kan matakin da gwamnatin jihar Edo ta dauka na yin karain kudin makarantan jami'ar Ambrose Alli, Ekpoma, da fiye da kaso 300.

Kungiyar Daliban Najeriya Ta Kasa (NANS) ta ce za ta nuna turjiya kan duk wani yunkuri na hana talakawa karatun jami'a a kasar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Jami'ar Ambrose Alli
“Ya Fi Karfin Talaka”: Jami’ar Ambrose Alli Ta Kara Kudin Makaranta Da Kaso 300 Hoto: @DubisHub
Asali: Twitter

Kungiyar daliban ta yi barazanar saka kafar wando daya da gwamnatin jihar idan har ba a yi wani abu don sake duba abun da ta bayyana a matsayin karin kudin makaranta na tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Bikin Babban Sallah: Abba Gida-Gida Ya Ba Daliban Kano Hutun Mako Guda Don Su Sha Shagali

Mataimakin shugaban kula da harkokin makarantu na NANS na kasa, Kwamrad Egbeahie Vanessa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni a Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Muna Allah wadai da halin gwamnan jihar kan ilimin jami'a a jihar da kudirinsa na son ganin ilimi ya fi karfin talaka da yan Edo masu rufin asiri da yan Najeriya baki daya.
"Cewa wannan gwamnati mai ci bata kafa koda harsashin gini ko guda ba a jami'ar jihar abun mamakoi ne.
"Shekaru ukun da suka gabata a jami’ar ya kasance ana ta cin zarafin ma’aikata da dalibai, ana ta tsoratarwa da kuma barazana ga duk wanda ya kuskura ya yi magana kan rashin bin ka’idojin da gwamnatin jihar Edo ke yi na yin kasuwanci da jami'o'in jihar a kaikaice."

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kungiyar Ma’aikata Ta Bukaci FG Ta Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, Ta Yabi Wasu Jihohi

Egbeahie ya zargi mukaddashin shugaban jami’ar, Farfesa Sonnie Asomwan Adagbonyin, da mahukuntan sa da nuna kyama ga dalibai.

Shugaban daliban ya kuma bukaci iyaye da dalibai da kada su yi gaggawan biyan kudin makarantar yayin da za a tattauna da gwamnatin jihar don janye karin kudin makarantar na tashin hankali.

Tsarin kudin Najeriya ya lalace karkashin Emefiele, Tinubu ya magantu

A wani labari na daban, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, ya bayyana sabon matsaya dangane da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Tinubu ya yi magana a yayin tattaunawa da yan Najeriya mazauna kasar Faransa da kasashen da Turai da ke makwabtaka a gefen taron Duniya a babban birnin kasar Faransa, Paris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng