Ayyuka Da Suka Yi Min Yawa Ne Ya Hana Ni Shiga Jirgin Zuwa Kasan Teku Da Ya Gamu Da 'Bala'i, Ned Nwoko
- Shahararren dan siyasa, Ned Nwoko ya bayyana yadda aka gayyace shi yawon bude ido na jirgin ruwa
- Nwoko ya ce babban amininsa Hamish Harding na daga cikin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwa
- Ya bayyana Harding a matsayin abokin kirki in da ya mika sakon ta'aziya ga iyalansa kan rashin da suka yi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Dan siyasa a Najeriya kuma biloniya, Ned Nwoko ya bayyana cewa yana daga cikin wadanda aka gayyata yawon bude ido na jirgin ruwan da ya nutse.
Nwoko ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram yayin nuna alhininsa ga abokinsa kuma dan kasuwa, Hamish Harding.
Nwoko ya bayyana irin yawata duniya da suka yi da Mista Harding wanda yana daga cikin wadanda suka mutu a jirgin ruwan da ya nutse, cewar Premium Times.
Mutane 5 ne suka mutu a jirgin ruwan yawon bude idon
An tabbatar da mutuwar Harding tare da abokansa yayin da suka je yawon bude karkashin ruwa don ziyartar buraguzan jirgin ruwan Titanic da ya nutse shekaru 111 da suka gabata.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Nwoko:
"Mista Harding ya gayyace ni yawon bude ido na wannan jirgi da ya nutse a kasan ruwa, amma saboda wasu ayyuka na kasa ban samu dama ba.
"Harding yana daga cikin wadanda muke bincike don kawo karshen cutar cizon sauro a Afirka."
Nwoko ya tuna sakon Mista Harding na karshe da yake gayyatarsa zuwa yawon bude idon, kafin tafiyarsu a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni.
Ned ya bayyana yadda Harding ya gayyace shi ziyarar
Nwoko har ila yau, ya mika sakon ta'aziya ga iyalan Mista Harding.
Ya kara da cewa:
"Ya na matukar sha'awar abin, sakonsa na karshe a ranar Lahadi shi ne za su yi tafiyar idan yanayi ya bari.
"Yana son yawon bude ido, ina mika ta'aziya ga matarsa da 'ya'yansa, tabbas munyi asarar iliminsa da kwarewa."
Mutum 5 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya A Hadarin Jirgin Ruwa A Kano
A wani labarin, akalla mutane biyar suka mutu a wani hadarin jirgin ruwa a jihar Kano.
A hadarin an yi nasarar kubutar da mutane 6 da ransu a Dam din kanwa cikin karamar hukumar Madobi.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi shi ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Asali: Legit.ng