FCTA Ta Gargadi Masu Kiwon Shanu A Titunan Birnin Tarayya Abuja
- Hukumar Kula da Muhalli a Abuja ta yi barazanar kame shanun makiyaya a birnin Tarayya
- Daraktan hukumar, Osi Braimah shi ya bayyana haka a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni a Abuja
- Braimah ya ce lokaci ya yi da za su kwace shanun tare da kai masu shanun kotu don daukar mataki
FCT, Abuja - Hukumar Kula da Muhalli ta Abuja (AEPB) ta yi barazanar kama makiyaya masu kiwon dabbobi a birnin Abuja.
Daraktan hukumar, Osi Braimah shi ya bayyana haka a ranar Juma'a 23 ga watan Yuni a Abuja yayin rangadi.
Daraktan ya ce yin kiwo a titunan babban birnin Tarayya ya sabawa doka kuma duk wanda aka kama da saba dokar ba zai ji da dadi ba, cewar Tribune.
Hukumar ta yi gargadin kama masu kiwo a Abuja
Ya kara da cewa hukumar ta yi zama ba sau daya ba da kungiyoyin makiyaya don dakile faruwar hakan nan gaba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Dole zamu dauki matakai masu tsauri don ganin birnin ya rabu da dabbobin makiyaya.
"Dokar hana kiwon dabbobi a Abuja a bayyane take, dokar ta hana kiwon dabbobi akan hanyoyin birnin da kuma hanyar filin jiragen sama."
Ya kara da cewa:
"Dole mu dabbaka wannan dokar, abin ya yi yawa yanzu, idan kana Abuja zaka ga dabbobi da shanu ko ina, wannan ba zai yiyu ba.
"Zamu sa tsauraran matakai wurin kwace shanun da kuma kai wadanda suka karya dokar zuwa kotu."
Ya koka yadda ake samun hatsari dalilin kiwon shanun
Braimah ya koka kan yadda kiwon shanun ke jawo hatsarurruka a cikin birnin da kewaye dalilin kiwon dabbobin, TheCable ta tattaro.
Ya bayyana cewa hukumar za ta dauki matakai masu tsauri don ganin sun tsabtace birnin daga dattin kiwon dabbobi.
Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Share Harabar EFCC Na Kwanaki 3 Saboda Damfara
A wani labarin, kotu da ke zamanta a Abuja ta yanke wa matashi share harabar EFCC na kwanaki uku.
Matashin mai suna Okwo Mark ana zarginsa da shigar bultu da damfarar mutane a matsayin jami'in FBI.
Alkalin kotun ya kuma yanke wa matashin daurin watanni uku ko biyan kudin tara N50,000.
Asali: Legit.ng