Kotu Ta Maido Shugaban Leken Asiri da Buhari Ya Kora Daga Aiki a Shekarar 2018
- Mohammed Dauda ya sake samun nasara a kan gwamnatin tarayya a shari’ar da ake yi a kotu
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da an sauke shugaban hukumar ta NIA ne ba tare da bin doka ba
- Alkali ya zartar da hukunci cewa a maida Ambasada Dauda kuma a biya shi hakkokinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Kotun daukaka kara mai zama a garin Abuja, ya maida Mohammed Dauda a kan kujerar Darekta Janar na hukumar NIA a Najeriya.
Rahoton Tribune ya ce Alkalin babban kotun na birnin tarayya ya ci tarar gwamnati, ya bukaci a biya Amb. Mohammed Dauda Naira miliyan 1.
Mai shari’a Peter Ige ya zartar da wannan hukunci a ranar Alhamis da yake sauraron shari’ar da hukumar NIA ta kasa ta dauka a gaban kotunsa.
Alkalin ya ce ya kamata a kyale Ambasada Dauda ya yi ritaya a wurin aikinsa kamar yadda dokokin kasa su ka tanada a maimakon a tsige shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Alkalin, babu wata hujja gaban kotun da ke nuna wanda ake tuhuma ya aikata wani laifi ko ya saba doka da ta cancanci a fatattake shi.
Karamar kotu tayi gaskiya
A dalilin haka, Peter Ige ya yi watsi da karar NIA, yana kuma mai tabbatar da hukuncin farko da aka yanke a kotun sauraron korafin ma’aikata.
A rahoton da aka samu daga VON, an ji cewa kotun ma’aikata mai zama a garin Abuja ya yanke hkunci cewa a dawo da Dauda a kan mukaminsa.
Bayan maida sa kan kujera, Alkali Olufunke Anuwe ya umarci hukumar NIA ta biya jami’in duka albashi da hakkokinsa tun daga Maris na 2018.
Karamar kotu ta tabbatar da cewa tsige tsohon shugaban ya ci karo da dokar da ta kafa NIA.
Hukuncin babban kotun Abuja
“A bar Dauda ya cigaba da aiki har ya yi ritaya kamar yadda dokokin kasa su ka tanada.
Babu hujja a gaban kotun nan da ta ke nuna cewa wanda ake tuhuma ya yi wani laifi ko ya saba wata dokar kasa.
Kotu ta yi watsi da karar nan saboda ba ta da karfi kuma ana tabbatar da hukuncin kotun ma’aikata"
- Alkalin kotu
Shari'ar zaben Gwamna
Ku na da labari cewa ana gwabza shari’a tsakanin PDP da Jam’iyyar APC mai-ci a kotun sauraron karar zaben Sokoto a kan zaben Gwamna da aka yi.
Shaidun da Sa’idu Umar zai gabatar sun hada har da wasu jami'an hukumar INEC. An fahimci rayuwar Lauyoyi da sauran shaidun PDP na ganin barazana.
Asali: Legit.ng