Cire Tallafi: TUC Ta Koka Yadda Gwamnoni Da 'Yan Majalisu Ke Sharholiya, Ba Talaka A Ransu, Ta Fadi Bukatunta

Cire Tallafi: TUC Ta Koka Yadda Gwamnoni Da 'Yan Majalisu Ke Sharholiya, Ba Talaka A Ransu, Ta Fadi Bukatunta

  • Shugaban Kungiyar Gamayyar 'Yan Kasuwa (TUC), Festus Osifo ya koka kan yadda 'yan siyasa ba su damu da halin da talakawa ke ciki ba
  • Osifo ya bayyana haka ne a ranar Laraba 21 ga watan Yuni a hirarsa da gidan talabijin na Channels a Abuja
  • Osifo ya ce yadda 'yan siyasa ke yawo a ayarin motoci ya tabbatar da cewa ba talaka a ransu bayan cire tallafin mai

FCT, Abuja - Shugaban Kungiyar Gamayyar 'Yan Kasuwa (TUC), Festus Osifo ya koka kan yadda 'yan siyasa ba su damu da matsalar cire tallafin mai akan talakawa ba.

Osifo ya bayyana haka ne a ranar Laraba 21 ga watan Yuni yayin hira da gidan talabijin na Channels inda ya ce 'yan siyasa ba su damu da halin da talaka yake ciki ba.

Kara karanta wannan

NAHCON Ta Ce Maniyyata 6,000 Ne Kadai Ba A Yi Jigilarsu Zuwa Saudiyya Ba, Ta Bayyana Dalilai

Cire Tallafi: TUC ta koka kan yadda 'yan siyasa ba su damu da halin da talaka ke ciki ba
TUC Ta Bukaci Gwamnati Ta Yi Wani Abu Kan Cire Tallafin Mai. Hoto: Tori News.
Asali: Facebook

Ya ce sai dai a gansu a 'Ayarin Motoci' ba iyaka duk da irin wahalhalun da talakawa ke sha dalilin cire tallafin man fetur.

TUC ta bukaci 'yan siyasa su kawo dauki kan cire tallafin

Osifo ya ce lokaci ya yi da ya kamata 'yan siyasa da manyan kasar su nemo hanyar da za su taimakawa talakawa, The Pledge ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Misali, ayarin motoci da zaka gani na gwamnoni da 'yan majalisu har yanzu babu abinda ya sauya, duk da wahalhalun cire tallafin mai."

Ya kara da cewa, a kwanakin baya kungiyar kwadago ta bukaci gwamnati ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000 daga N30,000 saboda yanayin tattalin arzikin kasar.

Ya ce mafi karancin albashi na N30,000 a shekaru biyar da suka gabata, ba komai ba ne idan aka kwatanta da yadda farashin kayayyaki suka tashi a yanzu.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Bode George Zai Koma Wajen Tinubu a APC? Gaskiya Ta Bayyana

Ya bayyana yadda talaka ke cikin mawuyacin hali

Ya kara da cewa:

"'Yan Najeriya na fama da matsanancin wahala a kasar wanda ya yi muni sosai.
"Kuna cewa mutane su daura damara, ku meye kuka yi a bangaren ku don taimakawa talakawa a matsayin ku na 'yan siyasa?
"Abin da muke fada shi ne lokacin da gwamnati ba ta iya biyan kudin tallafi me ta ke yi da kudin?.
"Dukkan kudaden da suke karba bashi na Naira Tirilian 23 me suke yi da su?."

Osife ya ce dole gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya bayanin yadda take kashe kudaden da take karba basuka.

Cire Tallafi: Dole A Kara Mafi Karancin Albashi Zuwa N200,000, TUC

A wani labarin, Gamayyar Kungiyar 'Yan Kasuwa (TUC) ta bukaci gwamnati ta kara mafi karancin albashi zuwa N200,000.

Kungiyar ta ce hakan ya zama dole duba da yadda gwamnatin ta cire tallafin man fetur a kasar.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Maganar Farko Da Ya Shiga Hannun Hukumar EFCC

Shugaban kungiyar, Festus Osifo shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa inda yace gwamanati ta duba tashin farashin kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.