Farfesa Ya Bukaci FG Ta Gudanar Da Kidayar Dabbobi Don Sanin Adadinsu, Ya Bayyana Amfanin Hakan Ga Tsare-Tsare

Farfesa Ya Bukaci FG Ta Gudanar Da Kidayar Dabbobi Don Sanin Adadinsu, Ya Bayyana Amfanin Hakan Ga Tsare-Tsare

  • Farfesa a fannin kimiyyar dabbobi ta jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo, Olajide Babayemi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gudanar da kidayar dabbobi
  • Farfesa Olajide ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridu a ranar Laraba 21 ga watan Yuni
  • Farfesan ya ce yadda kidayar mutane ke da muhimmanci haka ma ta dabbobi ke da amfani wurin sanin adadin dabbobin a kasar

Jihar Oyo - Farfesa Olajide Babayemi na jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da kidayar dabbobi don sanin adadinsu.

Farfesan wanda kwararre ne a kimiyyar dabbobi ta tsangayar noma ya bayyana haka yayin wata hira da yan jaridu a ranar Laraba 21 ga watan Yuni a Lagos.

Farfesa ya bugaci FG ta gudanar kidayar dabbobi a kasar
Farfesa Ya Bukaci FG Ta Gudanar Da Kidayar Dabbobi. Hoto: Colorado Public Radio.
Asali: Facebook

Ya ce yadda babu ainihin adadin dabbobin, kidayar za ta taimaka wurin tsare-tsare da ya shafi dabbobin, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tinubu: Tsare-Tsaren Sabon Shugaban Najeriya Na Daukar Idon Duniya – Birtaniya

Ya bukaci Tinubu ya gudanar da kidayar dabbobi

Ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya ba da fifiko a harkar noma a kasar, ya ce akwai iri da dabbobi da za su taimakawa harkar noma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Idan ana maganar samar da abinci, ana nufin noma kenan, ya kamata Tinubu ya mai da hankali a harkar noma.
"Tinubu ya kamata kuma ya mai da hankali wurin kidayar dabbobi saboda sanin adadinsu a kasar.
"Kamar yadda kidayar mutane ke da muhimmanci haka ma na dabbobi, ba mu san adadinsu ba sai dai tsammani.

Farfesan ya bayyana yadda ake cewa akwai shanu 12m da awaki 40m ya ce waye ya fadawa mutane haka?.

Shin an taba yin kidayar dabbobi?

Ya kara da cewa kamar yadda rahotanni suka tattaro:

"Misali, idan muna da shanu 24m a Najeriya, ka raba adadin da mutanen Najeriya kaga nawa zai bayar.

Kara karanta wannan

An Ba Abba Gida-Gida Wa’adin Awanni 72 Ya Dakatar Da Rushe-Rushe a Kano, Cikakken Bayani

"Tun yaushe aka yi kidayar dabbobi, ba wanda zai fada, ban ta ba ganin an yi ba tun da aka haifen, ba a taba yi ba."

Farfesa Ya Shawarci 'Yan Najeriya Su Rungumi Kiwon Kwadi Don Samun Abinci

A wani labarin, wani Farfesa ya shawarci 'yan Najeriya da su rungumi kiwon kwadi don samun arziki.

Farfesa Moshood Mustapha na tsangayar ilimin halittar dabbobi na jami'ar Ilorin da ke jihar Kwara shi ya bayyana haka.

Ya ce kiwon kwadi yana matukar samar da arziki musamman ganin yadda kifi ya yi tsada a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.