Sabbin Bayanai Sun Nuna Jihar Imo Ce Ke Kan Gaba Cikin Jerin Jihohin Da Man Fetur Ya Fi Tsada

Sabbin Bayanai Sun Nuna Jihar Imo Ce Ke Kan Gaba Cikin Jerin Jihohin Da Man Fetur Ya Fi Tsada

  • Sabbin bayanai da hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta fitar sun nuna ƴan Najeriya sun siya man fetur da tsada a watan Mayun 2023
  • Bayanan sun nuna cewa an siyar da litar man fetur akan farashin aƙalla N238.11 a faɗin ƙasar a watan na Mayu
  • A jihar Imo nan ne farashin man fetur a watan Mayu ya fi na ko ina tsada daga nan sai jihohin Gombe da Jigawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa farashin da aka siyar da man fetur ya ƙaru da kaso 37.57% daga kan N173.08 a watan Mayun 2022 zuwa N238.11 a watan Mayun 2023.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahoton sanya ido kan farashin man fetur wanda ta sanya a shafinta na yanar gizo, sannan Legit.ng ta samo shi a ranar Talata, 20 ga watan Yunin 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sabon Shugaban Yan Sandan Najeriya Ya Kama Aiki Gadan-Gadan Bayan Gaje Baba

Jihohin da man fetur ya fi tsada a watan Mayun 2023
Farashin man fetur a watan Mayu Hoto: NBS
Asali: Facebook

A cewar rahoton kuɗin da masu ababen hawa a ƙasar nan suka biya a watan Mayun 2023 ƙarin kaso 7.57% ne idan aka kwatanta da abinda suka biya a watan Mayun 2022 (N173.08 ), Punch ta rahoto.

Sai dai, hukumar NBS ta bayyana cewa farashin man fetur a watan Mayun 2023 ya ragu da kaso 6.28% idan aka kwatanta da farashin N254.06 da aka siyar da shi a watan Afirilun 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani ɓangare na rahoton NBS ɗin na cewa:

"A ɓangaren bayanan jihohi, jihar Imo tana da farashin da ya fi kowane tsada na man fetur na N300.00, daga nan sai jihar Gombe mai N299.77 da jihar Jigawa mai N297.50."
"A ɓangare ɗaya kuma birnin tarayya Abuja ya samu farashi mafi ƙaranci na N195.00, daga nan sai jihar Niger mai N201.82 da jihar Plateau mai N203.33."

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Matar Da Ta Farfado Ana Shirin Kaita Makwanci Ta Sheka Da Gaske

Haka kuma bayanan sun nuna cewa yankin Kudu maso Gabas ya samu farashi mafi tsada a wayan Mayun 2023 na N256.64, yayin da yankin Arewa ta tsakiya ya samu farashi mafi arha na N208.74.

Jerin jihohi 10 da farashin man fetur ya fi tsada a watan Mayu

  • Imo - N300.00
  • Gombe - N299.77
  • Jigawa - N297.50
  • Taraba - N295.00
  • Kebbi - N286.40
  • Enugu - N287.67
  • Kaduna - N280.00
  • Rivers - N250.42
  • Zamfara - N243.27
  • Lagos - N213.89

Farashin Lantarki Zai Lula Sama

A wani labarin kuma, akwai yiwuwar farashin shan wutar lantarki ya karu da fiye da 40% nan da wata mai zuwa. Hakan ya na nufin an soke duk wani tallafin shan wuta.

Hakan na zuwa ne bayan an daidaita farashin kuɗaden waje a ƙasar nan wanda gwamnatin Shugaba Tinubu ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng