'Yan Sanda Sun Cafke Kasurgumin Dan Fashi Kwanaki 3 Da Samun Yancin Shan Iska Daga Gidan Kaso
- Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta sake kama wani kasurgumin dan fashi da ya addabi mutane a yankin jihar
- Wanda ake zargin mai suna Kingsley dan shekaru 45 bai wuce kwanaki uku da fitowa daga gidan gyaran hali na Ikoyi ba
- Jami'an 'yan sandan sun ce Kingsley bayan fitowarsa ya nemo abokansa don ci gaba da ayyukan sace-sace
Jihar Lagos - Rundunar 'yan sanda ta sake kama wani kasurgumin dan fashi kwanaki uku da sake shi daga gidan gyaran hali na Ikoyi a jihar Lagos.
Wanda ake zargin mai suna Kingsley dan shekaru 45 an kama shi ne da wasu 'yan fashin a yankin Ijora Badia da ke jihar.
Rundunar 'yan sandan ta tabbatar da cewa Kingsley bai wuce kwanaki uku da fitowa daga gidan gyaran hali ba aka sake kama shi yana aikata wani laifi.
'Yan sanda sun tabbatar da kama dan fashin
Bincike ya tabbatar da cewa fitowar Kingsley ke da wuya sai ya nemo abokan cin mushe a yankin don ci gaba da ayyukan sace-sace, cewar Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kama wanda ake zargin a ranar Talata 20 ga watan Yuni.
Ya kara da cewa an kama Kingsley da abokansa ne suna tsaka da yin fashi da makami a ranar Asabar 17 ga watan Yuni, Daily Trust ta tattaro.
Hundeyin ya bayyana yadda aka kama kasurgumin dan fashin
Hundeyin ya ce jami'ansu da ke ofishin yanki na Ijora Badia sun gudanar da samamen ne da misalin karfe 9:30 na dare a yankunan Ijora da Apapa.
A cewarsa:
"Jami'an mu da ke ofishin yanki na Ijora Badia sun gudanar da samame na musamman wanda ya yi sanadiyar kama 'yan fashin a yankin Ijora Badia da Apapa.
"Daya daga cikin wadanda aka kaman akwai Kingsley wanda bai wuce kwanaki uku da fitowa daga gidan gyaran hali na Ikoyi ba.
"Sauran wadanda ake zargin ba su wuce shekaru 19 da 25 ba, an kama su suna yin fashi ga masu motoci akan hanya."
Hundeyin ya ce za a mika wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an gama bincike.
Jami'an Tsaro Sun Cafke Wani Mai Gadi Da Ya Hada Baki Da Abokinsa Suka Fasa Gidan Da Yake Aiki
A wani labarin, 'yan sanda sun kama wasu matasa da suka hada baki da yin fashi da kuma sata a Lagos.
Daya daga cikin wadanda ake zargin mai gadi ne a gidan da aka yi satar inda ake zargin ya hada baki da wasu don fasa gidan.
Mai gadin Pius, ya kira wani abokinsa mai suna Tony don aikata fashin tare da fasa gidan da yake gadin.
Asali: Legit.ng