Tserewa Zai Yi: Gwamnati Ta Haskawa Kotu Hadarin Bada Belin Godwin Emefiele

Tserewa Zai Yi: Gwamnati Ta Haskawa Kotu Hadarin Bada Belin Godwin Emefiele

  • Godwin Emefiele ya dauki kwana da kwanaki ya na tsare a wajen jami’an tsaron DSS a Najeriya
  • Tsohon Gwamnan bankin CBN ya shiga da kara a kotu, ya na ganin hukuma ta shiga hakkinsa
  • Ma’aikatar shari’a da jami’an tsaro sun fadawa Alkali cewa Emefiele zai kufce idan ya samu beli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Hukumar tsaro ta farar kaya watau DSS, ta shaidawa babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja hikimar cigaba da tsare Godwin Emefiele.

Punch ta ce Godwin Emefiele ya na kalubalantar tsare shi da jami’an DSS su ke cigaba da yi.

Hukumar DSS ta sanar da babban kotun kasar cewa tsohon Gwamnan na babban bankin kasa na CBN zai tsere daga Najeriya ne muddin aka ba shi beli.

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele Hoto: Getty Images/Dia Dipasupi
Asali: Getty Images

Jami’an tsaro sun bayyana Emefiele a matsayin barazana ta fuskar hawa jirgin sama ya bar Najeriya yayin da ake kokarin cigaba da bincike a kan sa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babbar Kotu Zata Yanke Hukuncin Kan Dakataccen Gwamnan CBN Emefiele

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon Gwamnan CBN a kotu

Ganin an dauki kwana da kwanaki ba tare da ya ga Lauyoyi ko ‘yanuwansa ba, Mista Emefiele ya shigar da kara a babban kotun mai zama a garin Abuja.

Ma’aikacin bankin ya shiga kotu ya na zargin hukumar tsaron da toye masa hakki. Lauyoyin DSS da na gwamnatin atarayya duk sun musanya zarginsa.

A raddin da su ka gabatarwa kotu, DSS da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya sun fadawa Alkali ana yi wa tsohon Gwamnan zargin ta’addanci.

Meye laifin Godwin Emefiele?

Jaridar ta rahoto cewa OAGF da DSS duk sun yi karin haske cewa ba saboda siyasa aka cafke ta’alikin kamar yadda wasu mutane su ke nunawa ba.

Lauyoyin gwamnati sun nesanta tsare Emefiele da yunkurin canza takardun kudi ko shiga siyasa, su ka ce zargin da ke wuyansa sun shafi ta’addanci ne.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

Har ila yau, OAGF ya ce zargin tallafawa kungiyoyin ta’addanci da wasu aika-aika na rashin gaskiya ba su cikin dalilan da su ka jawo aka garkame shi.

Kwanaki 10 Emefiele yana tsare

Awanni bayan Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamnan babban bankin, sai aka ji labari hukumar DSS ta cafke shi, tun lokacin har yau ya na hannu.

Rahoto ya zo cewa Shugaban kasa Tinubu ya kuma bada umurnin a cigaba da bincike kan abubuwan da Emefiele ya aikata lokacin yana gwamnan CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng