Za a Rasa Janarori 100 a Gidan Soja a Sakamakon Nade-naden Bola Tinubu

Za a Rasa Janarori 100 a Gidan Soja a Sakamakon Nade-naden Bola Tinubu

  • Taoreed Lagbaja, Emmanuel Ogalla da kuma Hassan Abubakar sun zama Hafsun sojoji a Najeriya
  • Sababbin shugabannin ne za su canji Farouk Yahaya, Awwal Gambo da Oludayo Amao a gidan soja
  • Abin da aka saba shi ne ‘yan ajin tsofaffin hafsoshin za su ba ‘yan bayansu wuri domin rike mukamai

Abuja - Kusan manyan sojoji 100 daga ciki har da Janar, Birgediya Janar da Air Vice Marshals da Admiral za su bar aiki saboda canji da aka samu.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin hafsoshin tsaro, Punch ta ce a dalilin haka ne za a ayi wa wasu manya-manyan sojoji ritayar dole.

Ritayar za ta shafi sojojin kasa, ruwa da na sama wadanda su ka samu sababbin shugabanni.

Sojoji
Sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: Getty Images/Micheal Kappeler
Asali: Getty Images

Baya ga ritaya da za a yi wa jami’an tsaron, da-dama daga cikinsu za su samu karin matsayi. Wannan ce al’ada a duk lokacin da aka samu canji.

Kara karanta wannan

Jirgin Bola Tinubu Ya Sauka a Faransa, An Ji Ranar da Shugaban Kasa Zai Dawo Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce hakan na zuwa ne bayan an yi wa Manjo Janar 24 da Birgediya Janar 38 ritaya a shekarar bara saboda sun yi shekara 35 su na aiki.

Hafsoshi za su samu karin girma

Manjo Janar Christopher Musa zai zama cikakken Janar, Taoreed Lagbaja zai koma Laftanan Janar, sai kuma Emmanuel Ogalla zai zama Admiral.

A karshe sabon shugaban hafsun sojin saman da aka nada zai koma Air Marshal Hassan Abubakar. Duk za ayi wannan ne bayan majalisa ta tantace.

Al'adar gidan Soja a Najeriya

A gidan soja idan karami ya samu matsayi, ya zama dole ayi wa na gabansa ritaya domin ba za ta yiwu ya karbi umarni daga wajen kaninsa a aiki ba.

An dauko hafsun tsaro ne daga ‘yan aji na 38 sauran kuma ‘yan aji na 39 a gidan soka ne. Hakan zai jawo jami’ai kusan 100 da ke gabansu, su yi ritaya.

Kara karanta wannan

Janar Taoreed Abiodun Lagbaja: Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hafsan Sojoji

Sojojin kasa, sama da na ruwa ‘yan aji na 37 da 38 za su ajiye khaki. Wata majiya ta ce dole adadin abokan karatunsu ya ragu yanzu saboda halin rayuwa.

An kafa tarihi a mulkin Tinubu

Rahoton da mu ka fitar ya nuna yadda mutumin Kudu maso yamma ya zama Shugaban Sojojin kasar nan a karon farko cikin shekaru fiye da 40.

Dogarin Bola Tinubu 1999 ya zama IGP, sannan jami'in da ya hana a tsere da $8m a filin jirgi ya gaji Hameed Ali, zai rike shugabancin hukumar Kwatsam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng