Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sabbin Hafsoshin Tsaro da NSA
- Shugaban ƙaaa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗa sabbin shugabannin hukumomin tsaron Najeriya
- A wata sanarwa da SGF ya rattaɓa wa hannu, Tinubu ya ƙara wa Nuhu Ribaɗu girma zuwa mai ba da shawara kan tsaron ƙasa (NSA)
- Haka nan ga naɗa shugabannin hukumomin sojin ƙasa, sama da na ruwa, ya naɗa IGP da shugaban hukumar tattara bayanan fasaha
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabbin shugabannin hukumomin tsaron Najeriya bayan sauke waɗanda suke kai yau Litinin.
The Nation ta rahoto cewa shugaban ya sanar da naɗin sabbin ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Jerin sunayen waɗanda zasu ja ragamar tsaron Najeriya
A wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen waɗanda shugaba Tinubu ya naɗa da kuma hukumomin da zasu jagoranta, ga su kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Malam Nuhu Ribaɗu - Mai bai wa shugaban ƙasa shawar kan harkokin tsaron ƙasa (NSA).
2. Manjo Janar C.G Musa - Babban Hafsan hafoshin tsaron Najeriya (CDS).
3. Manjo T. A Lagbaja - Shugaban hukumar sojin ƙasa a Najeriya (COAS).
4. Rear Admiral E. A Ogalla - Shugaban hukumar sojojin ruwa ta ƙasa.
5. AVM H.B Abubakar - Shugaban hukumar sojin saman Najeriya.
6. DIG Kayode Egbetokun - Muƙaddashin sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP).
7. Manjo Janar EPA Undiandeye - Shugabar hukumar tattara bayanan fasaha ta ƙasa.
A ɗazu mun kawo muku rahoton cewa shugaba Tinubu ya sallami baki ɗaya hafsoshin tsaro, sufetan yan sanda, masshawarta, da shugahan kwastam daga bakin aiki.
A rahoton da Daily Trust ta kawo, sanarwan ta bayyana cewa wannan mataki zai fara aiki ne nan take daga yau Litinin, 19 ga watan Yuni, 2023.
Tinubu Ya Nada Hadiza Bala da Hannatu Musawa Cikin Sababbin Masu Bada Shawara
A wani rahoton na daban kun ji cewa Shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara naɗa sabbin masu ba shi shawara ta musamman.
Mai girma shugaban kasa ya zabi Hadiza Bala Usman a matsayin mai bada shawara a wajen kula da tsare-tsare. Ya kuma naɗa Hannatu Musa Musawa.
Asali: Legit.ng