IMF Tayi Alkawarin Taimakon Najeriya Ganin Gyare-Gyaren da Bola Tinubu Ya Kinkimo

IMF Tayi Alkawarin Taimakon Najeriya Ganin Gyare-Gyaren da Bola Tinubu Ya Kinkimo

  • Hukumar IMF ta yi farin ciki da tsarin da aka fito da shi na daidaita farashin kudin kasashen ketare
  • Ari Aisen ya bayyana cewa za su taimakawa Najeriya domin a karfafi tattalin arziki idan akwai bukata
  • IMF ce mai bada lamuni a Duniya, ta dade ta na bada shawarar a fito da wannan tsari, amma ba ayi ba

Abuja - IMF mai bada lamuni ta Duniya ta jinjinawa Najeriya a kan matakin da ta dauka na barin farashin kudin kasar waje hannun ‘yan kasuwa.

Babban bankin Najeriya ya sanar da ruguza sabanin da ake da shi a farashin kudin ketare, This Day ta ce hakan ya jawo hukumar IMF ta yabi kasar.

Wakilin IMF a Najeriya, Ari Aisen ya fitar da jawabi a makon da ya gabata, ya na mai nuna cewa a shirye hukumarsu ta ke da ta taimakawa Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Tinubu Ya Girgiza Najeriya Cikin Makonsa Na 3 a Matsayin Shugaban Najeriya

Shugaban kasa
Bola Tinubu a kujerar Shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

An yi aiki da shawarar IMF

Mista Aisen yake cewa sun dade da bada wannan shawara kuma a dalilin haka sun ware kudi da nufin ganin wannan tsari da aka fito da shi ya yi nasara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin shawarwarin da IMF ta ba Najeriya a watan Fabrairun nan akwai janye tallafin fetur wanda sabuwar gwamnati ta dauki wannan shawara.

Legit.ng Hausa ta fahimci masana har da tsohon Gwamnan CBN sun goyi bayan a soke mabambatan farashin da ake da su wajen cinikin kudin waje.

Darektocin IMF su na ganin hakan zai fayyace manufar gwamnati, ya ba ‘yan kasuwa kwarin gwiwa zuba hannun jari, ya karfafa arzikin kasar.

Karfafa cin gashin-kan CBN da tsaida darajar ruwa ya na cikin shawarwarin da aka bada, haka zalika an bukaci a dauki matakin rage hauhwar farashi.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Ba Mazauna Garuruwa Makamai Domin Yakar ‘Yan Bindiga a Arewa

Naira ta na mikewa a kasuwa

Arise TV ta ce hakan na zuwa ne a lokacin da Naira ta kara daraja daga N702/$1 zuwa N663/$1.

Dalar Amurka ta rasa kusan N10 kenan daga lokacin da aka fito da tsarin da ya daidaita farashin kudin kasar waje zuwa ranar da aka tattara labarin.

Osinbajo zai jagoranci tawagar Commonwealth

An samu labari za a zabi Shugaban kasa da 'Yan Majalisa a Sierra Leone a Yunin nan, wannan ne zabe na biyar bayan dawowa mulkin farar hula.

Wanda yake jagorantar kungiyar Commonwealth wajen sa ido a zaben shi ne Yemi Osinbajo. Farfesan ne ya jagoranci NEC a gwamnatin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng