Gwamnan Oyo Ya Fame Gyambon da Ya Kusa Warkewa, Ya Ce Ba Atiku Bane Mai Son Hada Kan ’Yan Kasa, Wike Ne

Gwamnan Oyo Ya Fame Gyambon da Ya Kusa Warkewa, Ya Ce Ba Atiku Bane Mai Son Hada Kan ’Yan Kasa, Wike Ne

  • Gwamnan jihar Oyo ya yiwa Atiku Abubakar ba’a ana tsaka da wani taro a jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya
  • Ana ‘yar tsama tsakanin gwamnonin G5 da dan takarar shugaban kasan PDP a zaben da ya gudana a kasar
  • Ana ci gaba da rigima tsakanin Wike da Atiku, hakan ya faro ne tun kafin zaben shugaban kasa na 2023

Jihar Ribas - Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya kara ruruta wutar rikicin da ke ci gaba da ci a jam’iyyar PDP, inda ya yi ba’a ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Gwamnan, a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron da aka shirya wa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal, ya bayyana shakkun akidar Atiku ta son hada kan ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Manya basu tsira ba: 'Yan ta'adda sun farmaki ayarin tsohon gwamnan PDP, an kashe dan sanda

An yi taron ne a a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni, inda Makinde ya kira tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin wanda ya alanta kansa a matsayin mai son hadin kan ‘yan kasa, amma yace Wike ne sahihin mai son hada kan jama’a.

Atiku ya sha suka daga gwamna Seyi Makinde
Dan takarar PDP Atiku da tsohon gwamna Wike | Hoto: Atiku Abubakar, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wani ya kira kansa Mr. Unifier [mai son hada kan ‘yan kasa], amma daga abin da na gani a cikin wannan gaskiyar, mai son hada kan ‘yan kasa na gaskiya shine Gwamna Nyesom Wike."

Alaka mai tsami tsakanin Atiku da gwamnonin G5

Idan baku manta ba, akwai rashin jituwa tsakanin dan takarar shugaban kasan PDP da wasu gwamnonin jam’iyyar biyar; ciki har da Wike da Makinde.

Ana kyautata zaton akwai tasirin gamayyar gwamnonin wajen faduwar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasan da ya gudana a Najeriya.

Kara karanta wannan

G5: Yadda Jagororin PDP Su Ka Yi Watsi da Jam’iyyarsu, Su Ka Bi APC a Zaben Majalisa

Yanzu dai Atiku ya fadi zabe, gwamna Wike da ‘yan tawagarsa na ci gaba da bayyana gamsuwarsu da mulkin Tinubu na APC.

Sabuwar rigima ta barke a bayan tsagin Wike ya yi nasara kan Atiku a wata yarjejeniya

Jam'iyyar PDP ta kara samu kanta cikin wani halin kakanikayi bayan sabuwar rigima ta barke a tsakanin tsagin Atiku Abubakar, da na Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Rivers.

Sabuwar rigimar ta ɓarke ne a dalilin goyon bayan Kingsley Chinda, wani babban na hannun daman Wike a mukamin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai da 'yan jam'iyyar PDP suka yi.

A cewar rahoton The Nation, Chinda ya zama dan takarar PDP ne ba tare da wani abokin hamayya ba a lokacin wani taro da 'yan majalisun jam'iyyar suka gudanar a birnin tarayya Abuja, a ranar Juma'a, 16 ga watan Yunin 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.