Tashin Hankali Yayin da Tsageru Suka Bindige Wani Yaro Dan Shekara 13 Tare da Sace an Sace Wani a Bauchi

Tashin Hankali Yayin da Tsageru Suka Bindige Wani Yaro Dan Shekara 13 Tare da Sace an Sace Wani a Bauchi

  • Rahoton da muke samu daga jihar Bauchi ya bayyana yadda aka harbe wani yaro a kasuwar Jama’are
  • An kuma tattaro yadda ‘yan bindigan suka sace wani mutum a harin da suka kai ranar kasuwar mako
  • Ya zuwa yanzu, ‘yan sanda sun labarta yadda lamarin ya faru da kuma irin matakin da suka dauka

Jihar Bauchi - Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kasuwar Jama’are da ke jihar Bauchi sun harbe wani yaro mai suna Khalifa Umar mai shekaru 13 har lahira.

Rahoton da muka samo daga gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da wani Alhaji Sama’ila Magaji tare da raunata wasu mutum biyu a daren ranar Asabar.

Wani mazaunin garin Jama’are ya ce mutane sun yi mamakin harin domin sabon abu ne a gare su kuma Jama’are ba ta da dazuzzukan da ke kusa da jama’a.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Makiyaya da manoma sun kaure a jihar Arewa, an hallaka mutum 13 nan take

Yadda aka hallaka wani yaro a Jama'are ta jihar Bauchi
Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Asabar ranar kasuwa ce kuma mun ga 'yan bindiga kusan 40 ko 50 a kan babura."

‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni.

A cewar Wakili ga Channels:

“Jiya, da misalin karfe 20:10:00 wato misalin karfe 8:10 na yamma wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun zo da yawa a kan babura.
“Sun mamaye kasuwar Jama’are suna harbin iska inda suka yi garkuwa da wani Alhaji Sama’ila Magaji, suka harbe wani Khalifa Umar mai shekaru 13 sannan suka raunata wani Mustafa Sabiu dan shekara 51 kana suka harbe shi a cinyarsa. Harsashin ya kuma gogi wani daga mai suna Rapheal na Chiboke a cikinsa.”

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Babban Malami a Arewacin Najeriya

Matakin da ‘yan sanda suka dauka

Bayan samun labari, rundunar ‘yan sandan ta tura jami’ai domin kai dauki ga mazauna da wadanda suka zo cin kasuwar.

Ya bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun je wurin da lamarin ya faru, inda suka ceto wanda ya jikkata kana suka zarce da shi asibiti.

A wajen da aikin ta’addancin ya faru, an gano kwanson harsasai guda hudu na AK 47, an kuma samu harsashin da ba a harba ba guda daya.

An tattaro cewa an ba da gawar wanda aka kashe ga iyalan don yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya zuwa yanzu dai jami’ai sun bazama domin tabbatar da tsaro da neman inda aka kai wanda aka sacen.

‘Yan NDLEA sun kwamushe rikakkun ‘yan safarar kwaya

A wani labarin, kunji yadda wasu tsagerun ‘yan safarar kwaya suka shiga hannun jami’an tsaro a wani yankin jihar Legas.

Wannan na zuwa ne a cikin watan Yuni, inda tuni aka gano yadda suke gudanar da barnarsu tsakanin Najeriya da Qatar.

Kara karanta wannan

Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike tare da kokarin gurfanar dasu a gaban kuliya manta sabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.