Bayan Mulki: Farfesa Pantami Ya Sake Karbar Lambar Yabo Ta Gwanintar Aiki Daga Gidan Talabijin A Abuja

Bayan Mulki: Farfesa Pantami Ya Sake Karbar Lambar Yabo Ta Gwanintar Aiki Daga Gidan Talabijin A Abuja

  • Farfesa Isa Ali Pantami, tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani ya samu lambar yabo daga gidan talabijin na Qausain
  • Mallam Nasir Musa Albanin Agege, shugaban hukumar gidan talabijin din shi ya mika wannan lambar yabo ta gwanintar aiki ga tsohon ministan
  • Ya ce Farfesan ya ba da gudunmawa marar misaltuwa ga harkokin sadarwa da kuma tattalin arziki na zamani a lokacin da yake rike da mukami

FCT, Abuja - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya samu lambar yabo ta gwanintar aiki daga gidan talabijin a Abuja.

Hukumar gidan talabijin ta Qausain bisa jagorancin shigabanta, Mallam Nasir Musa Albanin Agege ne ta ba shi wannan lambar yabo a Abuja.

Farfesa Pantami ya samu lambar yabo ta gwanintar aiki
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami. Hoto: Channels TV.
Asali: Twitter

Agege ya ce sun ba shi wannan lambar yabo ne saboda gudumawar da ya bayar a lokacin da yake kan kujerarsa ta minista, cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shin EFCC Ta Ayyana Neman Matawalle Ruwa A Jallo? Gaskiya Ta Fito

Agege ya Farfesa Pantami ya kawo ci gaba a bangarori da dama a karkashin ofishinsa

Ya kara da cewa wannan lambar yabo an ba shi ne do ganin irin sauyi da ya kawo a ma'aikatarsa da kuma ci gaba a harkan tattalin arziki na zamani a lokacinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Wannan lambar yabo an bai wa tsohon ministan ne saboda irin abubuwan ci gaba da ya kawo da suka bunkasa tattalin arzikin kasar a zamanance."

Farfesa Pantami ya nuna jin dadinsa game da lambar yabon da aka ba shi

Yayin da yake karbar lambar yabon, Farfesa Isa Pantami ya godewa hukumar gidan talabijin din bisa wannan karimci da suka nuna masa, PM News ta tattaro.

Ya nuna kwarin gwiwar cewa tabbas kasar na kan hanya na amfani da tattalin arziki na zamani don inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: Gwamnan Arewa Ya Samo Mafita, Za a Fara Jigilar Dalibai a Jiharsa Kyauta Ba Ko Kobo

Farfesa Pantami Ya Fara Shirye-Shiryen Sauka Daga Kujerar Ministan Sadarwa

A wani labarin, Farfesa Ali Isa Pantami ya fara shirye-shiyen tattara kayansa don barin ofishin ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani.

Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami shi ne tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani wanda ya fito daga jihar Gombe.

Wannan na zuwa kwanaki kadan da gwamnatin Buhari ke shirin tafiya bayan shafe shekaru takwas akan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.