Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci a Jihar Ondo

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci a Jihar Ondo

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da babban limamin masallaci a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade
  • Tsagerun sun farmaki malamin addinin ne a gonarsa da ke yankin Uso sannan suka tisa keyarsa zuwa wani wuri da ba a sani ba
  • A halin da ake ciki, maharan sun tuntubi iyalinsa amma ba su bukaci kudin fansa ba

Ondo - Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da da babban limamin masallacin Uso da ke karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade.

An tattaro cewa yan bindigar da yawansu ya kai biyar sun sace malamin addinin mai shekaru 67 a gonarsa.

Malamin addini da yan bindiga suka sace
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci a Jihar Ondo Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an sace malamin ne da misalin karfe 3:00pm a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni a Asolo Farm Camp, da ke garin Uso.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun bude kafar zantawa da yan uwan malamin da abun ya ritsa da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maharan sun tuntubi dangin malamin

Majiyar ta fada ma manema labarai cewa basu riga sun bukaci kudin fansa ba amma dai sun sanar da yan uwanda da su nemo "kudi mai kyau" domin ceto malamin.

Majiya ta ce:

"Sun tuntubi iyalin jim kadan bayan sun yi garkuwa da shi, suna masu sanar da iyalin cewa yana tare da su amma basu riga sun bukaci kudin fansa ba."

Ya kara da cewar an kai rahoton lamarin zuwa ofishin yan sandan Uso.

A halin da ake ciki, an tattaro cewa an fara taron addu'o'i na musamman a masallacin da ke garin domin neman Allah ya dawo da malamin lafiya.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da take martani, kakakin rundunar yan sandan jihar, Misis Funmilayo Odunlami sannan ta ce jami'an rundunar da yan sa kai suna a daji suna neman malamibn, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Bayyana Abun Da Wadanda Suka Kafa Boko Haram Suka Fada Masa Game Da Tushen Ta’addanci

Ta ce:

"Da misalin karfe 6:00pm na yau (Asabar), an kai wani rahoto hedkwatar Uso, cewa babban limamin Uso ya je gonarsa da safe sannan kuma bai dawo ba, daga bisani mutanensa suka bi gonar, sun ga waya da motarsa amma ba su ga mutumin ba, DPO da jami'ansa da yan sa kai suna daji a yanzu haka don gano inda mutumin yake."

6 daga cikin daliban Unijos 7 da yan bindiga suka sace sun shaki iskar yanci

A wani labari na daban, mun ji cewa shida daga cikin daliban jami'ar Jos bakwai da aka yi garkuwa da su sun samu yanci bayan shafe kwanaki biyu a tsare.

An yi garkuwa da daliban wadanda ke zama a wajen makaranta a daren ranar Laraba a dakunansu da ke yankin Ring Road a karamar hukumar Jos ta arewa da ke jihar Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng