Hajjin Bana: Dubban Maniyyata Sun 'Makale' A Filin Jiragen Saman Legas

Hajjin Bana: Dubban Maniyyata Sun 'Makale' A Filin Jiragen Saman Legas

  • Maniyyata aikin hajji masu haramar zuwa Saudiyya da dama sun makale a filin jiragen saman kasa da kasa na Murtala Mohammed a Lagos
  • Mafi yawa daga cikin maniyyatan masu tafiya ne ta jiragen yawo yayin da kamfanonin suka dau hayan kamfanin Arik Air don jigilar maniyyatan
  • Mahajjatan sun durfafi ofishin Arik Air da aka ce zai yi jigilarsu don sanin dalilin ba ta musu lokaci yayin da ake daf da rufe filayen jiragen Saudiyya

Jihar Lagos - Dubunnan maniyyata aikin hajji zuwa Saudiyya sun makale a filin jiragen saman Murtala Mohammed da ke Lagos.

Mafi yawan wadanda suka makalen sun hada da maniyyata masu tafiya ta jiragen yawo na Kungiyar Hajji da Umrah (AHUON).

Maniyyata sun makale a filin jiragen saman Lagos
Maniyyatan Da Suka 'Makale' A Filin Jiragen Saman Legas. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Yayin da kamfanin jiragen yawon suka dauki hayar kamfanin jiragen sama na Arik tun jigilar maniyyatan zuwa Saudiyya.

Kara karanta wannan

An Zabo Mana Bala'i: Kanawa Sun Fusata Da Rushe-Rushen Abba, Sun Hana Rushe Gidajensu

Cikin fushi maniyyatan sun durfafi ofishin Arik Air suna zanga-zangar rashin daukarsu zuwa kasa mai tsarki akan lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, mahajjata da dama suna makale a cikin filin jiragen, yayin da wasu ke bacci tun kwanaki hudu da suka wuce don jiran lokacin da za a dauke su.

Kamfanonin jiragen yawon sun dauki hayar jiragen Arik Air don jigilar maniyyatan yankin Kano da Lagos da kuma Abuja.

Maniyyatan sun koka cewa suna tsoron kada su rasa damar zuwa kasa mai tsarki ganin ana daf da rufe filayen jiragen saman Saudiyya.

Daya daga cikin maniyyatan ya shaidawa Daily Trust cewa mafi yawansu an shirya jigilarsu tun 14 ga watan Yuni, amma har yanzu suna filin jirgi.

Maniyyatan suna kwana a masallatai da budadden fili wanda har harabar filin jiragen sun cika babu masaka tsinke, cewar Independent.

Kara karanta wannan

Tsadar Man Fetur: Gwamnan Arewa Ya Samo Mafita, Za a Fara Jigilar Dalibai a Jiharsa Kyauta Ba Ko Kobo

An Tura Maniyyata Zuwa Aikin Hajji a Saudi Su Kadai Saboda Rashin Biyan Kudi

A wani labarin, maniyyatan aikin hajji daga jihar Plateau suna tsoron kada su samu matsala saboda rashin kudi, wanda hakan ka iya samar da matsala a ibadarsu.

Mahajjatan suka ce malamai da masu kula da lafiya da aka saba turawa, bana ba sa tawagar raka su zuwa kasar Saudiyya ba tare da sun san dalili ba.

Ana zargin cewa tsohuwar gwamnatin Simon Lalong da ta shude bata kai kudaden mahajjatan ba kafin mika muli zuwa sabuwar gwamnatin Caleb Mutfwang.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.