Hajjin 2023: Gwamna Uzodimma Ya Daukin Nauyin Mahajjata 200 Zuwa Saudiyya
- Gwamnatin jihar Imo ta dauki nauyin Musulmai 200 zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali a aikin Hajjin 2023
- Gwamna Hope Uzodimma ya jagoranci kaddamar da gidan gwamnatin jihar Imo a Owerri, inda ya karbi mutane 200 da suka amfana da shirin
- An tattaro cewa wannan shine karo na farko cikin shekaru 10 da gwamnatin jihar Imo za ta dauki nauyin Musulmai zuwa aikin Hajji
Imo, Owerri - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya kaddamar da shirin zuwa Makkah, kasar Saudiyya ga maniyyata a jihar domin aikin hajjin 2023.
Da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar da ke Owerri, Gwamna Uzodimma ya bukaci Musulmai 200 da za su aikin Hajji a jihar da su zamo jakadun kirki na jihar sannan su nuna dabi'ar kwarai.
Gwamnan ya yaba ma al'ummar Musulmi a jihar kan fahimtarsu sannan ya sake basu tabbacin ci gaba da samun zaman lafiya ga kowa.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun yi amafani da damar wajen yi wa gwamnan addu'a da jinjina masa kan taimaka masu da yi a niyansu na sauke farali da kuma walimar da ya shirya masu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zuwa aikin hajjin Musulmai a jihar Imo shine irinsa na farko cikin shekaru 10 - Wani da ya amfana
A cewar daya daga cikin wadanda suka yi magana:
"Ni kadai ne zan je aikin hajji a Ideato, wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyi."
Sun kara da cewar kimanin fiye da shekaru 10 kenan da wata gwamnati za ta dauki nauyin aikin hajji.
Yayin da suke ba gwamnan tabbacin samun goyon bayansa a kudirinsa na zarcewa kan kujerarsa, sun kuma eoki Allah ya samar da taimakon da yake bukata domin zarcewa a matsayin gwamnan jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Jirgin mahajjatan Jigawa ya yi saukar gaggawa a Kano
A wani labarin kuma, mun ji cewa wani jirgin sama mai tafiya kasar Saudiyya ya tsallake rijiya da baya inda ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano bayan injin dinsa ya samu matsala a sama a yammacin ranar Laraba, 31 ga watan Mayu.
Jirgin na kamfanin Max Air Limited da lamba, Max B747-HMM yana dauke da rukunin farko na maniyyata aikin hajji 554 daga garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa zuwa Saudiyya domin aikin hajjin 2023.
Asali: Legit.ng