Jerin Mutum 12 Da Shugaba Tinubu Yakamata Ya Bincika, Tsohon Dan Majalisa Ya Bayyana
- Muhammed Kazaure Gudaji ya bayyana jerin wasu jami'an gwamnati da ake zargi da cin hanci wanda ya ce yakamata a bincike su
- Gudaji ya ce dole ne Shugaba Bola Tinubu ya binciki mutanen idan har yana son ya farfaɗo da tattalin arziƙi
- Tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa idan aka ƙwato kuɗaɗen da ke hannunsu, za su taimaki ƙasar nan sosai
Abuja - Tsohon ɗan majalisa Muhammed Gudaji Kazaure, ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya binciki irin su Hadiza Bala Usman, tsohuwar shugabar hukumar Nigerian Ports Authority (NPA), da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, idan har da gaske yake wajen ƙwato kuɗaɗen da aka sace.
A cewar rahoton The Cable, Gudaji ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni a cikin shirin Brekete Family.
"Mutanen da dole Tinubu ya bincikesu domin farfaɗo da tattalin arziƙi", Gudaji
Gudaji wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, ya lissafo wasu tsaffi da masu riƙe da muƙamai a yanzu da ya kamata a bincikesu. Ya ya bayyana cewa mutum 12 ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Akwai mutane 12 da shugaban ƙasa yakamata ya bincika. Na farko, idan muna son mu farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan, yana da kyau a cafke tare da bincikar gwamnan CBN, wanda yanzu haka ake bincikensa."
"Na biyu, shugaban hukumar EFCC. Sannan idan muna bincikar shugaban EFCC, a gayyato Magu tsohon shugaban hukumar, domin ya kawo wasu abubuwan da ya bari a ofishin domin ya yi bayani."
"Na uku, shugaban kamfanin NNPC. Na huɗu tsohon ministan shari'a, Malami. Na biyar, Sabiu Yusuf Tunde, wanda yake sakatare na musamman ga tsohon shugaban ƙasa Buhari."
Bayan Ganawa da Tinubu, Asri Dakubo Ya Tona Asirin Wasu Sojoji Da Ke Ɗaukar Nauyin Ɓarayin Mai a Najeriya
Cikakken jerin sunayen da Gudaji Kazaure ya ambato
1. Godwin Emefiele - dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
2. Abdulrasheed Bawa - dakataccen shugaban hukumar ƴaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC).
3. Mele Kyari - Shugaban kamfanin man fetur na (NNPCL).
4. bubakar Malami - tsohon ministan shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa.
5. Sabiu 'Tunde' Yusuf - sakatare na musamman ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
6. Muhammad Nami - shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa (FIRS).
7. Bashir Yusuf Jamoh - babban darektan hukumar Nigerian Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA).
8. Mohammed Bello-Koko - Babban manajan hukumar tashoshin jiragen ruwa ta ƙasa (NPA).
9. Hadiza Bala - tsohuwar shugabar hukumar NPA.
10. Sadiya Umar Farouq - tsohuwar ministaɓ jinƙai, kiyaye annoba da jindaɗin al'umma.
11. Ibrahim Magu - tsohon shugaban EFCC.
12. Dukkanin mataimakan gwamnan CBN na yanzu waɗanda suka yi aiki tare da Emefiele.
Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:
Gaskiya Kan Bidiyon Dala Da Ake Danganta Emefiele Da Shi
A wani labarin, gaskiya ta bayyana kan bidiyon daloli wanda ake danganta dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da shi.
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da gaskiyar inda bidiyon ya fito, kuma tabbas kuɗaɗen da ake ƙirgawa a cikin bidiyon bana Emefiele ba ne.
Asali: Legit.ng