Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Asari Dakubo da Wasu Jiga-Jigai a Villa
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi bakunci tsohon ɗan fafutukar neman sauyi a yankin Neja Delta, Asari Dakubo, a Villa
- Dakubo ya isa fadar shugaban ƙasa da karfe 11:00 na safiyar ranar Jumu'a kuma daga zuwa ya shiga ganawar sirri da Tinubu
- A kwanakin baya, an ji Dakubo na cewa yan Najeriya su tuhume shi idan har gwamnatin Tinubu ta gaza yin abinda ya dace
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na ganawa yanzu haka da tsohon ɗan tawaye a yankin Neja Delta, Asari Dokubo, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Dakubo ya isa fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Jumu'a kuma daga zuwa ya shiga ganawar sirri da shugaba Tinubu.
Mako uku da suka gabata, Mista Dakubo, ya tattara matasan Neja Delta kuma ya jagorance su suka halarci zaman Kotun sauraron korafe-korafen zaɓen shugaban ƙasa mai zama a Abuja.
Ku tuhume ni da laifi idan gwamnatin Tinubu ta gaza - Dakubo
Ya kasance ɗan amutun masoyin shugaban ƙasa Tinubu kuma ko a ranar Alhamis da ta gabata, ya gaya wa 'yan Najeriya cewa su kama shi da laifi idan har gwamnatin Tinubu ta gaza.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma kare shugaban kasan kan cire tallafin ƙan fetur, matakin da ya ɗauka tun a jawabinsa na ranar rantsarwa 29 ga watan Mayu, 2023.
Ya ce tsoffin shugabannin Najeriya, Goodluck Jonathan, da Muhammadu Buhari sun gaza yin abinda shugaba Tinubu ya aiwatar cikin 'yan makonni da hawa kan madafun iko.
Channels tv ta rahoto Dakubo na cewa:
"Idan Ahmed Bola Tinubu ya gaza, ya baku kunya to ku kama ni da laifi, ba zan ba kowa hakuri ba. Na san waye shi tun 1992 kuma na san abinda ya tsayu a kai."
"Ƙuma zan iya shiga tsakaninsa da mutane na faɗi haka. Wannan ne matakin da ɗan uwana Jonathan ya gaza ɗauka lokacin da ya samu dama, haka Buhari amma Tinubu ya yi a ranarsa ta farko."
Cikakken Jerin Ministocin da Ake Tsammanin Tinubu Zai Nada Gabanin 28 Ga Yuli
A wani rahoton kuma Mun kawo muku jerin Ministocin da ake tsammanin shugaba Tinubu zai miƙa wa majalisa gabannin ranar 28 ga watan Yuni, 2023.
Sabuwar dokar da Muhammadu Buhari, ya rattaɓa wa hannu ta nuna duk sabon shugaban da ya zo, yana da watanni 2, watau kwanaki 60 ya miƙa sunayen ministoci ga majalisa.
Asali: Legit.ng