Tinubu: Yadda Aka Jawowa Aliko Dangote Asarar Naira Tiriliyan 1.45 Cikin Kwana 2

Tinubu: Yadda Aka Jawowa Aliko Dangote Asarar Naira Tiriliyan 1.45 Cikin Kwana 2

  • Abin da babban mai kudin Najeriya da Afrika, Aliko Dangote ya mallaka a Duniya ya ragu sosai
  • Dukiyar Attajiran kasar nan ta yi kasa a ‘yan kwanakin nan, ana zargin tsarin CBN ya kawo haka
  • Shugaban kamfanin na Dangote Group ya rasa $3.12bn, a kudin Najeriya adadinsu ya zarce N1tr

Abuja - Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya yi asarar makudan kudi a halin yanzu. Ana zargin hakan bai rasa nasaba da tsarin bankin CBN.

Bayanan da aka samu daga alkaluman attajiran Duniya na Bloomberg (BBI), ya nuna manyan masu kudin Duniya sun rasa dukiya mai yawa.

BBI sun yi suna wajen fitar da jerin mutanen da suka fi kowa kudi a Duniya tare da yin bayanin silar arzikinsu da yadda dukiyarsu ke motsawa.

Dangote da Bola Tinubu
Aliko Dangote da Bola Tinubu Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Bayanan da aka samu a shafin Bloomberg a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni 2023 ya tabbatar da cewa arzikin Attajiran Najeriya ya ragu yanzu.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abin ya taba masu kudi

Watakila daga cikin wadanda canjin ya fi yi wa tasiri akwai shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote wanda ya fi kowa arziki.

The Cable ta ce Aliko Dangote ya rasa dukiyar da ta kai Dala biliyan $3.12 a yanzu.

Idan aka yi lissafi a farashin kudinmu na Najeriya, adadin abin da Dangote ya rasa ya kai tsakanin Naira Tiriliyan 1.4 zuwa Naira Tiriliyan 2 a yau.

Legit.ng ta ce a ranar Litinin, an wayi gari Dangote ya mallaki $20.9bn, zuwa Laraba sai aka ji arzikinsa ya karye, ya sauka zuwa Dala biliyan 17.8.

CBN ya saki Naira a kasuwa

Jaridar ta ce ana zargin ba komai ya jawo hakan ba illa sauyin da aka yi a kasuwar canji na soke bambace-bambace a farashin kudin kasashen waje.

Kara karanta wannan

Gajerun Bayanai a Kan Mutane 8 Da Tinubu Ya Nada a Matsayin Masu Bada Shawara

Kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawari tun tuni, babban bankin CBN ya saki darajar Dalar Amurka ta rika yawo a kasuwar canji.

Abin da sabon tsarin yake nufi shi ne Gwamnatin Najeriya ba ta da hannu a kan tsaida farashin kudin waje, sai yadda ‘yan kasuwa su ka yi ciniki.

Shugaban BUA ya tabu

Tasirin bai tsaya ga Dangote kadai ba, abin ya shafi Abdussamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA Group ya rasa kusan $2.73bn daga cikin dukiyarsa.

Rahoton da mu ka samu ya ce rashin dukiyar da Alhaji Rabiu ya yi, ya jawo ya yi ƙasa daga matsayin da yake kai, an samu attajirai 200 sun hau gaban sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng