Matata Ta Gudu Ta Kara Wani Aure Daban, Miji Ya Nemi Saki a Kotu
- Wani ɗan kasuwa a birnin tarayya Abuja ya maka matarsa a gaban Kotu bisa zargin ta ƙara sabon aure a kan aure
- Magidancin mai suna, Chuka Emmanuel, ya nemi Kotu ta raba aurensu kuma ta ba shi izinin ci gaba da kula da yaransu guda uku
- Ya ce tun 2020 matarsa ta gudu daga gida ba tare da izini ba, daga baya ya gano har ta ƙara aure kuma ta haihu
Abuja - Wani magidanci ɗan kasuwa, Chuka Emmanuel, ya kai ƙarar matarsa mai suna Jane gaban Kotun Kostumare da ke zama a Jikwoyi a babban birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.
Ɗan kasuwan ya maka mai ɗakinsa a gaban Kotun ne bisa zargin ta ƙara wani sabon aure a sirrance duk da tana a matsayin matarsa, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.
A bayanin da ya yi cikin ƙarar da ya shigar, Mista Chuka, ya shaida wa Kotun cewa:
"Matata ta sa ƙafa ta bar cikin gidana kuma ba tare da neman izini na ba, daga bisani na gano wurin da ta koma, lokacin da na je wurin sai na fahimci ta kara auren wani daban kuma har ta haihu da shi."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Saboda wannan abu da ta aikata ne ya sa nake rokon Kotu ta datse igiyoyin aurenmu kowa ya kama gabansa."
Ɗan kasuwan ya faɗi lokacin da matar ta gudu
Ɗan kasuwan ya ƙara da cewa matarsa ta gudu ta barshi da rainon 'ya'yan da suka haifa su 3 tun shekarar 2020.
"Tun wannan lokaci ni nake kula da 'ya'yanmu, bana son wani ya zo ya gurɓata musu tunani su guje ni, ina rokon wannan Kotu ta hana matata zuwa ganin 'ya'yana a gida idan bana nan."
"Kuma ina rokon wannan Kotu mai adalci ta tsinka igiyoyin aurenmu kuma ta bani ikon kula da 'ya'yana," inji mijin.
Wane mataki Kotun ta ɗauka?
Bayan sauraron ƙorafin mai shigar da ƙara, Alkalin Kotun mai shari'a Labaran Gusau, ya sanar da ɗage ƙarar zuwa ranar 22 ga watan Yuni, kamar yadda PM News ta tattaro.
Kyakkyawar Budurwa Ta Damfari Wani Matashi Da Ya Ce Yana Sonta, Ta Bar Shi Da Cizon Yatsa
A wani rahoton na daban kuma Wani matashi ya koka bayan wata budurwa ta damfare shi sannan ta goge shi ta yadda ba zai iya tuntuɓarta ba har abada.
Ta tura masa lambar asusun ajiyarta na banki inda nan da nan cikin tsuma da ɗoki ya tura mata kuɗi ba tare da sanin cewa zai yi nadamar hakan ba.
Asali: Legit.ng