Sojojin Najeriya Sun Kwato Tsabar Kudi Naira Miliyan 11 Daga Hannun Yan Boko Haram, Sun Aika Da Dama Barzahu
- Sojojin Najeriya sun sanar da ƙwato sama da naira miliyan 11, sun kuma halaka, tare da kama ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da suka kai wa 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin sun kai hare-haren ne a ƙauyuka, maɓoya, sansanoni, da wuraren horarwar na 'yan ta'addan a ƙauyuka, tsaunuka, da gefen ruwa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe
- Sojojin ƙasa, sama da na ruwa na ‘Operation Hadin Kai’ sun yi aiki tuƙuru wajen kakkaɓe ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun ayyuka a shiyyar Arewa maso Gabas
Abuja – Sojojin Najeriya sun sanar da ƙwace sama da naira miliyan 11, sannan kuma sun halaka tare da kame ‘yan ta’adda da dama a hare-haren da suka kai.
Sojojin sun kuma ƙwace makamai a samamen da suka kai a kauyuka, maboya, sansanoni da wuraren atisaye a ƙauyuka, tsaunuka da bakin ruwa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe cikin makonni biyu da suka gabata.
Yadda Sojojin suka gudanar da aikin
Hedikwatar tsaron Najeriyar ta bayyana hakan ne a lokacin da take ƙarin haske kan yadda jami'anta ke gudanar da yaƙi da 'yan ta'addan Boko Haram da na Daular Islama ta yammacin Afirka (ISWAP), da sauran masu aikata laifuka a yankin Arewa maso Gabas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Manjo janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan, a taron manema labarai kan ayyukan rundunar a Abuja.
Danmadami ya ce sojojin ƙasa, sama da na ruwa na ‘Operation Hadin Kai’ na ci gaba da ƙoƙarin kakkabe ‘yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun ayyuka a yankin Arewa maso Gabas.
Sojojin sun halaka 'yan ta'adda da dama, gami da ƙwato makamai masu yawa
Ya ce a yayin farmakin da sojojin suka kai, sun halaka ‘yan ta’adda da dama, sun kuma kama wasu tare da ƙwato makamai masu yawa.
Ya ce sojojin ƙasan sun kwato kayayyaki da dama da suka haɗa kuɗi naira miliyan 11.04, sannan sun halaka ‘yan ta’adda 20, tare da kama wasu bakwai daban.
Ya ƙara da cewa, jami'an sun yi nasarar kama mutane 40 da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda kayan aiki, sannan kuma an kama gungun masu aikata laifuka su 15.
Sauran waɗanda Danmadami ya ce an kama sun haɗa da masu safarar miyagun ƙwayoyi guda hudu, masu garkuwa da mutane uku, da kuma ‘yan ta’adda uku.
Wani ɓangare na kalamansa da muka samu daga PM News na cewa:
“Sojoji sun ceto fararen hula 15 da aka yi garkuwa da su, yayin da ‘yan ta’adda 743 da iyalansu, wadanda suka hada da manya maza 42, manya mata 251 da ƙananan yara 452 suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban a cikin aikin da hukumar ke yi.”
Danmadami ya ce sojojin sama sun kai hare-hare ta sama a kauyen Tagoshe, inda suka bude wuta kan ‘yan ta’addan da ke boye a karkashin bishiyoyi da makamai masu linzami.
Ya ce bayanan sun nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata kayayyakinsu a harin da aka kai ta sama.
Gwamna Zulum na Borno ya ƙara wa'adin ritayar malaman asibitin jihar
Legit.ng ta kawo muku labarin cewa gwamnatin jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Babagana Umar Zulum, ta amince da ƙarin shekarun aje aikin ma'aikatan lafiya a jihar.
Gwamna Zulum ya amince da ƙara wa'adin aje aikin ma'aikatan lafiyar daga shekaru 60 zuwa 65 da haihuwa ga kowane mutum ɗaya.
Asali: Legit.ng