Tinubu Ya Shigo da Sabuwar Doka, Ana Sa Ran Mutane 500,000 Za Su Samu Aiki
- Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a kudirin kare bayanai, tuni ta zama doka da za tayi aiki a Najeriya
- Shugaban kasar ya yi alkawarin yin hanyar da mutum miliyan 1 za su samu aiki a wannan bangare
- Wannan mataki da Tinubu ya dauka zai yi sanadiyyar da kusan mutum 500, 000 za su samu na abinci
Abuja - A farkon makon ne Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a kudirin kare bayanai wanda tuni ta zama doka mai aiki a Najeriya.
Kamar yadda rahoto ya fito daga Leadership, kimanin mutane 500, 000 ake sa ran za su amfana da wannan doka, su samu ayyukan yi a kasar nan.
Hanyoyin da dokar za ta rage marasa aikin yi sun hada da horas da jami’an kare bayanai da bada lasisi ga kamfanonin tabbatar da bin doka.
Wadannan kamfanonin da za a kafa, za su yi aiki da masu kula da bayanai da masu sarrafa shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rattaba hannu a kan kudirin har ya zama doka ya na daga cikin alkawuran da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jama’a a lokacin da yake neman zabe.
Alkawari ya cika
Da yake neman zama shugaban kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin magance zaman kashe wando, ya ce zai samar da ayyuka miliyan daya a fannin.
Tattalin arziki na zamani ya na cikin fannonin da matasa za su iya shiga domin neman arziki.
Jami'an NDPM sun yi karin haske
Babban jami’in bangaren tabbatar da shari’a da bin dokoki na NDPB, Babatunde Bamigboye, ya fitar da jawabi ya na mai wannan bayani a jiya.
A cewar wani babban kwamishina a NDPB, Dr. Vincent Olatunji dokar da aka shigo da ita za ta tabbatar da ‘yancin ‘yan kasa a kafar yanar gizo.
Baya ga samun ‘yanci, dokar za ta kare sirrin masu yin cefane ta kafafen yanar gizo na zamani. Gidan rediyon Najeriya ya fitar da wannan labari.
Jonathan a Aso Rock
Rahoto ya zo cewa Dr. Goodluck Jonathan ya yi zaman farko da Bola Ahmed Tinubu bayan hawansa kujerar mulki karshen watan Mayun 2023.
Tsohon Shugaban Najeriyan wanda ya bar ofis a 2015 ne Kungiyar ECOWAS ta nada domin ya sasanta rikicin siyasar kasar Mali da ake fama da shi.
Asali: Legit.ng