Maniyyata 156 Daga Kano Ba Za Su Samu Damar Yin Aikin Hajjin Bana Ba, Hukumar Alhazai Ta Ba Da Dalili
- Alhazai 156 daga jihar Kano ne ba za su samu zuwa ƙasa mai tsarki don gudanar da aikin hajjin bana ba, saboda sayar da kujerun da jami’an hukumar suka yi fiye da kima
- Hukumar Alhazai ta ƙasa, ta warewa Kano kujeru 6144, amma hukumar ta jihar ta siyar da ƙarin kujeru 156, wanda hakan ya sa wasu maniyyatan rasa damar yin aikin hajjin na bana
- Darakta janar na hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano, Laminu Rabiu, ya sanar da cewa za a gudanar da bincike bayan aikin hajji domin hukunta jami’an da ke da hannu wajen aikata hakan
Kano - Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kano ta bayyana cewa aƙalla maniyyata 156 ne za su yi hasarar zuwa ƙasa mai tsarki a bana sakamakon sayar da kujerun da jami’an hukumar suka yi da ya wuce adadi.
Hukumar Alhazai ta ƙasa ta warewa Kano kujeru 6144 ne, amma wasu jami'an hukumar na jihar Kano, sun siyar da ƙarin kujeru 156, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Za a bincika jami'an hukumar Alhazan da suka aikata hakan
Babban daraktan hukumar, Laminu Rabiu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai ranar Laraba a Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa za a binciki jami’an da ke da hannu a lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala aikin hajjin na bana.
Ya kuma yi kira ga waɗanda abin ya shafa da su yi haƙuri, inda ya ba su tabbacin cewa za a sanya su a cikin sahun farko na waɗanda za su je aikin hajji na baɗi.
A halin da ake ciki, maniyyata 2558 ne kawai hukumar ta yi jigilar su zuwa ƙasa mai tsarki yayin da take jiran jiragen da hukumar Alhazai ta kasa za ta bai wa jihar nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
A cewarsa:
“An ware wa jihar Kano 6144. Lokacin da na fara aiki bayan naɗa ni a matsayin darakta janar, na gano cewa sakatare na lokacin ya sayar da dukkan kujerun. Ban tarar da kujera ko ɗaya ba.”
“Bugu da kari, ya sayar da ƙarin kujeru 156, wanda hakan ke nufin ba za su samu damar yin aikin hajji ba duk da sun biya kuɗi kuma sun cika dukkan sharuɗan da ake bukata.”
"Abin takaici ne sosai a karɓi kuɗaɗen mutane, sannan a watsa musu ƙasa a fuska, bayan sun sanar da kowa da kowa cewa za su halarci aikin hajji."
Ba a bai wa wasu maniyyatan kujerun wasu ba
Ya kara da cewa sun bai wa maniyyatan haƙuri, sannan suka jaddada musu cewa sune sahun farko a aikin hajjin baɗi.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za su gudanar da bincike gami da hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin bahallatsar.
A karshe ya yi watsi da zarge-zargen da wasu ke yi na cewa an ɗauki kujerunsu an bai wa wasu, inda ya ce dama tuntuni kujerun sun riga da sun ƙare, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Kwana 5 kaɗai Alhazan Najeriya za su riƙa yi a Madina
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa a baya, Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa kwanaki biyar kawai Alhazan Najeriya za su riƙa yi a Madina sai su wuce zuwa Makkah.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon yawan ƙorafe-ƙorafen cunkoson Alhazan Najeriya da ake samu a birnin na Madina.
Asali: Legit.ng