Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'ar UNIJOS Guda 7, Sun Nemi Kudin Fansa

Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'ar UNIJOS Guda 7, Sun Nemi Kudin Fansa

  • Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace ɗaliban jami'ar UNIJOS 7 da daren jiya Talata
  • Rahoto ya nuna maharan sun shiga gidan kwanan ɗalibai na wajen makaranta da tsakar dare lokacin ɗaliban na cikin karatun jarabawa
  • Hukumar yan sanda ta tabbatar da kai harin kuma ta ce jami'anta sun mamaye jeji don ceto waɗanda aka yi garkuwa da su

Jos, Plateau State - Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da ɗaliban jami'ar tarayya da ke Jos (UNIJOS) guda 7 ranar Talata da tsakar dare.

The Nation ta fahimci cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na dare a daidai lokacin da ɗaliban suka tashi suna karatu domin jarabawar zango na biyu da suka fara.

Kofar shiga jami'ar UNIJOS.
Yan Bindiga Sun Sace Daliban Jami'ar UNIJOS Guda 7, Sun Nemi Kudin Fansa Hoto: UNIJOS

An tattaro cewa maharan sun kwashi ɗaliban daga gidan kwanansu mai zaman kansa da ke kusa da makarantar Nigerian School of Accountancy a gefen titin Bauchi, karamar hukumar Jos ta arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Rukunin Mutane 5 Da Ta Haramtawa Amfana Da Rancen Kuɗin Karatun Dalibai

Yan bindigan sun kai farmaki Hostel ɗin kana suka ɓalle kofar ɗakin da ɗaliban ke karatu, suka tilasta masu shiga cikin motar da suka zo da ita, sannan suka gudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ɗalibin da ke zaune a Hostel ɗin da abun ya auku, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa maharan sun tsare ɗaliban da bindigu kusan mintuna 30, gabanin su fito da su da tsiya.

Ya ce duk da sauran ɗaliban sun san da zuwan yan bindigan amma ba bu wanda ya iya hitowa har maharan suka gama suka yi gaba.

Wane mataki aka ɗauka zuwa yanzu?

Ɗalibin ya ƙara da cewa tuni suka sanar da hukumar 'yan sanda da kuma shugabannin jami'r Jos abinda ya faru.

Wasu bayanai sun nuna cewa jami'ar ta tura wakilai kuma sun ziyarci gidan ɗaliban da lamarin ya faru domin tattara bayanai, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Kudirin Bai Wa Ɗaliban Najeriya Bashin Kuɗi

Masu garkuwan sun kira waya, sun nemi kuɗin fansa

Wata majiya mai kusanci da ɗaya daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su, ta ce 'yan bindiga sun kira waya, sun nemi kuɗin fansar da har yanzu ba'a faɗi adadinsu ba.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, wanda ya tabbatar da sace ɗaliban, ya ce jami'ai sun bazama farauto maharan da kubutar da yaran.

Matasa Sun Barke da Zanga-Zanga a Birnin Tarayya Abuja Kan Rikicin Majalisa

A wani labarin kuma Wasu gungun matasa yan asalin jihar Nasarawa sun ɓalle da zanga-zanga a hedkwatar hukumar yan sanda ta ƙasa da ke Abuja.

A cewar shugabannin masu wannan zanga-zanga sun zabi yin haka ne domin nuna takaicinsu kan abinda ke faruwa a majalisar dokokin jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262