Yan Sanda Sun Yi Ram Da Matasa 5 Da Suka Lakadawa Mata Da Mijinta Duka A Abuja
- An gurfanar da wasu matasa 5 a gaban wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Karu Abuja, bisa zarginsu da cin zarafin maƙwabcinsu da matarsa
- Waɗanda ake tuhuman Abuchi Njoku, Rejoice Njoku, Chidera Njoku, Nwanchukwu Chidera, da Mary Nwanchukwu, sun amsa laifin da suka aikata a lokacin da ‘yan sanda ke bincikarsu
- Sai dai mutanen da ake tuhumar sun musanta zargin a gaban kotu wacce ta bayar da belinsu kan naira 100,000 kowannensu tare da kawo nagartaccen mutum guda ɗaya ya tsaya musu
Abuja - A ranar Larabar da ta gabata ne, rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu matasa biyar a gaban wata kotu mai daraja ta ɗaya da ke Karu a Abuja, bisa zargin su da yi wa maƙwabcinsu da matarsa dukan tsiya.
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Abuchi Njoku, Rejoice Njoku, Chidera Njoku, Nwanchukwu Chidera da Mary Nwanchukwu duka waɗanda ke zaune a Jikwoyi Phase III, Abuja da laifin haɗa baki da ji wa magidantan rauni.
Magidancin ya kai ƙararsu wajen 'yan sanda
Lauyan masu shigar da kara, Mista Ade Adeyanju, ya shaidawa kotun cewa Anthony Okafor ne ya kai ƙarar waɗanda ake tuhuma, kan farmakin da suka kai masa shi da matarsa Ngozi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa a yayin da ‘yan sanda ke bincikarsu, waɗanda ake tuhumar sun amince da aikata laifin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Mai gabatar da ƙara ya ce Okafor ne ya kai rahoton lamarin, a ofishin ‘yan sanda na Jikwoyi da ke Abuja.
Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 79 da na 240 na kundin laifuffuka na ƙasa.
Waɗanda ake tuhuma sun musanta zargin
Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin a gaban kotun.
Alkalin kotun, Malam Umar Mayina ya sanar da ba da belin waɗanda ake tuhuma a kan kuɗi naira 100,000 kowannensu, tare da kuma kawo mutum ɗaya da zai tsaya musu.
Ranar Dimokuradiyya: Dalilai 5 Da Suka Sa Ranar 12 Ga Watan Yuni Ke Da Muhimmanci A Tarihin Najeriya
Alƙali ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Yuni.
Gwamnan Kogi ya kori da muƙarabbansa guda 3
A wani labarin na daban, da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta cewa, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya kori kwamishinan noma na jihar da wasu muƙarrabai guda 2.
Sanarwa dai ta fito ne daga sakatariyar gwamnatin jihar ta Kogi, wacce ba ta yi wani cikakken bayani ba kan haƙiƙanin dalilin dakatarwar.
Asali: Legit.ng