Sai Na Ga Bayanku: Sabon Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Babban Tanadin Karar Da ’Yan Bindiga
- Gwamnan jihar Niger, Umar Bago ya sha alwashin kawo karshen 'yan bindiga don samun zaman lafiya
- Bago ya bayyana haka ne a ranar Litinin 12 ga watan Yuni a Abuja bayan kai ziyara fadar shugaban kasa
- Gwamnan ya ce sun yi hadaka da jami'an tsaro don kawo tsaro da kuma ci gaba da harkar ma'adinai a jihar
Jihar Niger - Gwamnan jihar Niger, Umar Bago ya koka kan yadda 'yan bindiga suka mamaye wurare da dama da ke da arzikin kasa a cikin jiharsa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin 12 ga watan Yuni a Abuja inda ya ce gwamnatinsa na kokarin samo wasu hanyoyi na samun kudin shiga ba tare da dogaro da gwamnatin Tarayya ba.
Bago ya ce sun hada kai da jami'an tsaro don kawo karshen 'yan bindiga
Har ila yau, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta hada kai da jami'an tsaro don kawo ingantaccen tsaro da kuma ci gaba da hakar ma'adinai a jihar nan da shekara mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bago ya yi wannan maganar ne kwana daya bayan 'yan bindiga sun hallaka akalla mutane 38 da kuma sace da dama a karamar hukumar Rafi da ke jihar, cewar Punch.
Bago ya kai ziyara ga Tinubu don taya shi murnar zaben shugabannin majalisu
Gwamnan ya kai ziyara ne wurin Shugaba Tinubu don taya shi murnan yin zaben shugabannin majalisu da ya ba Godswill Akpabio nasara a matsayin shugaban majalisar dattawa da kuma Tajudden Abbas a matsayin kakakin majalisar wakilai.
A cewarsa:
"Muna da arzikin kasa a jiharmu wanda ke da alaka da rashin tsaro. Mafi yawan inda kuke ganin 'yan bindigan nan akwai zinare a wurin, yawancin wadannan ayyuka su ke sa 'yan bindiga ke kara addabar mutane.
"Har ila yau, zamu yi amfani da arzikin da muke da shi, ba sai mun zo Abuja kullum muna karbar kudi ba, dole muyi amfani da arzikin da muke da shi wurin kawo ci gaba a jiharmu.
"Muna aiki tare da jami'an tsaro don tabbatar da dakile wannan rashin tsaro, da yardar Allah za mu yi nasara.
"Za mu yi hadaka da kamfanonin hakar ma'adinai don yin amfani da arzikin da jihar ke da shi, ina tabbatar muku da cewa zuwa shekara zamu cimma burinmu.
Gwamna Ya Karbe Filin da Aka Ba Jami’ar Janar Ibrahim Babangida
A wani labarin, gwamnatin jihar Niger ta kwace takardun mallaka da aka ba wa jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
Baya ga jami'ar gwamnatin Umar Bago ta kuma kwace takardun mallakar fili da aka ba wa wasu kamfanoni.
An kafa jami'ar ne a Lapai a 2005 wanda tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida ya mallaka.
Asali: Legit.ng