Awanni da Dakatar da Godwin Emefiele, Naira Ta Kara Yin Daraja a Kasuwar Canji

Awanni da Dakatar da Godwin Emefiele, Naira Ta Kara Yin Daraja a Kasuwar Canji

  • Bayan ta fadi war-was, yanzu Naira tayi hobbasa mai karfi daga N767 zuwa N754 a hannun ‘yan canji
  • A ranar Litinin dinnan da ta gabata, an fahimci Dalar Amurka ta karye da fiye da 10 a kasuwar BDC
  • Watakila hakan bai rasa alaka da matakin da Bola Tinubu ya dauka na dakatar da Gwamnan CBN

Abuja - A farkon makon nan Naira ta zabura a kasuwar ‘yan canji, sannan farashin kudin Najeriyan bai karye ba a hannun babban bankin CBN na kasa.

The Nation ta ce an samu wannan canji ne kwanaki kadan da barin Godwin Emefiele daga ofis a sakamakon dakatar da shi da Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Daga N767/$1 da aka saida Dalar Amurka a karshen mako, sai da mutane su ka yi cinikin kudin kasar wajen kan N754/$1 a ranar Litinin da ta gabata.

Kara karanta wannan

DSS ta Raba Emefiele da Fasfon Fita Kasar Waje, Za a Binciki Ofishi da Gidajensa

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: @Cenbank
Asali: Twitter

Tasirin dakatar da Gwamnan CBN?

A cikin kwanaki biyu, Dala ta rasa N13 a kan darajar ta ga Naira. Wasu su na ganin hakan bai rasa nasaba da matakin da shugaban kasa ya dauka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Mista Godwin Emefiele, kuma ya yi umarni a bincike shi, yanzu haka Gwamnan na CBN yana tsare.

‘Yan kasuwar canji su na sa ran hanyar da aka kama mai bullewa ce, za a gyara tattalin arziki.

A kafar I & E ta samun kudin waje, an rika saidawa mutane Dala ne a kan N463.38/$. Kusan haka farashin yake har ga masu sha’awar saida Dalolinsu.

Abubuwa sun canza farat daya

Business Day ta ce canjin da aka samu a CBN ya jawo rudani a kasuwa, a sanadiyyar haka ne Dala tayi tsadar da ba a taba gani ba a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Wasa farin girki: Yadda tun farko Tinubu ya hango Emefiele na masa tuggu a zaben 2023

Shugaban kungiyar ‘yan canji na ABCON a Najeriya, Ahaji Aminu Gwadabe, ya shaida cewa canjin da aka samu a CBN ne ya yi tasiri a kasuwar.

Daga Asabar zuwa yanzu, abubuwa sun sake zani. Ahaji Aminu Gwadabe ya na sa ran dakatar da gwamnan bankin ya jawo abubuwa su yi sauki.

Kamar yadda ‘dan kasuwar ya bayyana, su na sa ran Naira ta cigaba da kara daraja a duk kasuwannin canji ganin yadda abubuwa su ke sauyawa.

A jiya kuwa an saye Dalar Pound kan N940/£1, mai neman saye kuwa zai biya N955/£1. Amma masu hasashe sun ce kudin Birtaniyan zai karye.

Binciken Gwamnan CBN

Da alama Godwin Emefiele ya shiga uku domin rahoto ya zo cewa jami'an DSS sun karbe takardunsa domin hana shi barin Najeriya a halin yanzu.

Dakataccen Gwamnan bankin CBN bai isa ya je ko ina ba, hukuma ta taso shi a gaba da bincike. Ana sa ran za a fara laluben ofis da duk wasu gidajensa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng