Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Rukunin Mutane 5 Da Ta Haramtawa Amfana Da Rancen Kuɗin Karatun Dalibai

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Rukunin Mutane 5 Da Ta Haramtawa Amfana Da Rancen Kuɗin Karatun Dalibai

  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya cika ɗaya daga cikin alƙawuran da ya ɗauka yayin yaƙin neman zabensa, na bai wa ɗalibai rancen kudi don yin karatu
  • Ma’aikatar ilimi ta ƙasa ce za ta gudanar da shirin lamunin, wanda ɗalibai marasa ƙarfi da suka yi rajista a manyan makarantu za su amfana
  • Dokar lamunin karatun ta kuma ƙunshi wasu hukunce-hukunce ga waɗanda suka gaza biya, kamar ɗauri da tara, don ƙarfafa biyan lamunin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya sanya hannu kan ƙudirin ba da lamuni na kuɗi ga ɗalibai, wanda akewa kallon wani gagarumin ci gaba wajen magance matsalolin kuɗi da wasu ɗaliban da ke neman ilimi mai inganci ke fuskanta.

Daga yanzu a ƙarƙashin sabuwar dokar, ɗaliban Najeriya za su samu lamuni marar ruwa domin tallafa musu a harkokinsu na ilimi, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

"Ana Min Barazanar Kisa": Asari Dokubo Ya Fallasa Masu Son Ganin Bayansa a Doron Duniya

Ma’aikatar ilimi ta ƙasa ce za ta gudanar da tsarin ba da kuɗaɗen lamunin, kuma ɗalibai marasa ƙarfi da suka yi rajista a manyan makarantun ƙasar nan ne kawai za su amfana da shirin.

Gwamnatin Tarayya ta fiti da sabon tsarin ba da rancen kudin karatu
Gwamnatin tarayya ta bayyana rukunin mutanen da ba za su amfana da tsarin rancen kudin karatu ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Cikakken bayani kan sabon lamunin karatu na ɗalibai

Dele Alake, mai magana da yawun Shugaba Tinubu ya bayyana cewa babban maƙasudin ƙudirin shine samar da hanyar zuwa manyan makarantu ga ‘yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi ta hanyar asusun lamuni na ilimi na Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a buƙaci ɗaliban da suka cancanta su nuna shaidar karatunsu kafin su samu damar karɓar lamunin.

Domin tabbatar da ingancin yadda za a riƙa ba da lamunin da kuma sa ido kan shirin, za a kafa kwamitin da ya kutnshi wakilai daga masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Wanda Shugaba Tinubu Zai Iya Ba Mukamin Ministan Kudi

Rukunin ɗaliban da ba su cancanci lamunin kudin karatun ba

Akwai rukunin wasu mutane da basu cancanci karɓar lamunin kudin karatun ba, kamar yadda jaridar Tribune ta harhaɗa.

1. Wanda duk aka tabbatar da cewa ya gaza biyan wani bashi da ya taɓa karɓa daga ko ina ne a can baya.

2. Wanda aka taɓa samu da laifin satar amsa a kowace makaranta ce a baya.

3. Wanda aka taɓa samu da aikata mummunan laifi, irin su rashin gaskiya ko zamba.

4. Duk wani wanda aka taɓa samu da laifin ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi.

5. Wanda aka taɓa samun iyayensa (mahaifi ko mahaifiya) da laifin ƙin biyan bashin karatu a baya ko ma duk wani nau'in lamuni da aka taɓa ba shi.

Hukunce-hukuncen da aka tanada ga waɗanda suka ƙi biyan lamunin karatun

A cikin ƙudirin lamunin karatun akwai hukunce-hukunce da aka tanada ga waɗanda suka ƙi biyan kuɗin.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na Kasa Ya Yi Muhimmin Kira Ga Shugabannin Majalisa, Ya Bayyana Hanya 1 Da Za Su Taimaki Tinubu

Duk ɗalibin da ya ƙi biyan basussukan karatun da ake binsa, zai iya fuskantar ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, ko tarar naira 500,000, ko kuma duka biyun.

Ranakun hutun da 'yan Najeriya za su mora a shekarar 2023

A wani labarin da legit.ng ta kawo muku a baya, mun tattaro muku duka kwanakin hutun da 'yan Najeriya za su mora a cikin wannan shekarar ta 2023.

Ranakun hutu dai wasu ranaku ne na musamman da aka ware don tunawa da wasu manyan abubuwa da suka faru a baya na farin ciki ko na alhini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng