Wata Sabuwa: Fastoci Sun Waigo Ga Tinubu da Wasu Bukatu, Sun Ce Dole ya Cika Musu Alkawari
- Fastocin majami'ar Katolika sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika musu alkawuran da ya dauka a baya
- Rabaran Ignatius Kaigama shi ya yi wannan kira a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni a majami'ar St. Augustine da ke Abuja
- Ya ce Tinubu ya yi musu alkawarin hada kan 'yan kasa da kawo zaman lafiya a tsakanin addinai guda biyu kafin zabe
FCT, Abuja - Babban Faston majami'ar Katolika na Abuja, Rabaran Ignatius Kaigama ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya cika alkawarin da ya dauka wa Fastoci yayin neman zaben shugaban kasa.
Kaigama ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi 11 ga watan Yuni a majami'ar St. Augustine da ke Sun City cikin birnin Tarayya Abuja.
Ya ce Fastocin sun yi zama da Bola Tinubu kwanaki kadan kafin zaben shugaban kasa inda suka koka kan hadin kan addinai a kasar, cewar Daily Trust.
Ya bayyana irin alkawarin da Tinubu ya yi musu kafin zaben shugaban kasa
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya yi alkawarin inganta hadin kai a tsakanin addinan guda biyu, kamar yadda Punch ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
" Bukatun mu a bayyane suke, musamman matsalolin da ke damun kasar.
"A matsayinsa na shugaban kasa yanzu dole ya samo wasu hanyoyi da za su samar da natsuwa a zukatan mutane wanda rashin yin hakan shi ke kawo gaba da rashin hadin kai a cikin al'umma."
alci da rashin nuna wariya shi kadai zai inganta zamantakewa a tsakanin addinan guda biyu
Ya kara da cewa:
"Lokaci ya yi da ya kamata ya samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai, musamman Kirista da Musulmai a kasar.
"Yin hakan zai samu ne kadai idan ya kwatanta adalci ba tare da nuna wariya ba a mulkinsa, yanzu shi kadai ya ke da ikon yin hakan."
CAN Ta Soki El-Rufai Kan Kalamansa, Ta Ce Maganarsa Ba Ta da Alaka da Musulmai
A wani labarin, kungiyar CAN reshen jihar Kaduna ta caccaki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai kan kalamansa na tikitin Musulmi da Musulmi.
Kungiyar ta ce El-Rufai ya na magana ne a karan kansa amma ba a madadin Musulmin jihar Kaduna ba.
Asali: Legit.ng