A Karon Farko, Shugaban Kasa Tinubu Zai Yi Wa ’Yan Najeriya Bayani a Ranar Litinin Da Safe
- Gobe ranar dimokradiyya, Bola Ahmad Tinubum shugaban Najeriya zai yiwa ‘yan kasa jawabi na farko tun bayan da ya hau mulki
- An ruwaito cewa, wannan ne karon farko da Tinubu zai yiwa kasa jawabi tun rantsar dashi da aka yi a watan Mayun da ya shude
- A jawabinsa na karbar mulki, Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur, lamarin da ya jawo cece-kuce da yawa a Najeriya
A taron tunawa da ranar Dimokradiyya ta 2023, Shugaba kasa Bola Tinubu zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasar a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023, da misalign karfe 7 na safe, Vanguard ta ruwaito.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Abiodun Oladunjoye ya fitar a ranar Lahadi, ta bukaci gidajen talabijin, rediyo, da sauran kafafen yada labarai da su hada kai don yada jawabin Tinubu.
Wannan shine karo na farko da shugaba Tinubu zai yiwa 'yan Najeriya bayani a hukumance tun bayan hawansa mulki mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
An rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu
Idan baku manta ba, an rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasan Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan kada kuri’un da ‘yan Najeriya suka yi a watan Faburairun da ya gabata, inda Tinubu ya lashe zaben, kamar yadda INEC ta bayyana.
Tun rantsar da Tinubu, bai fito ya yi jawabi ba, baya ga jawabin da ya yi a filin rantsar dashi da aka yi, inda ya bayyana wasu daga cikin manufofi da sabbin abubuwan da gwamnatinsa ke tafe dasu.
Tinubu ya janye tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki
Shugaban Majalisar Dattawa: Rahoto Ya Nuna Yan Majalisa Na Iya Siyar Da Kuri’unsu $5,000, $10,000 Ko Fiye da Haka
A bangare guda, a ranar da aka rantsar da Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ba za ta iya ci gaba da ba da tallafin mai ba ga ‘yan kasar duba da wasu matsaloli na tattalin arziki.
A tun farko, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi yunkurin cire tallafin, amma daga bisani ya fasa, inda ya bar wa Tinubu wannan aiki mai tsauri.
Har yanzu, ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana rashin jin dadin yadda shugaban kasar a zuwa daya ya janye tallafin da ‘yan kasa ke mora na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng